"Za mu Karawa Abokan Hada Hadarmu Farashi", Masu Sana'ar POS
- Masu sana’ar hada hadar kudi ta POS a babban birnin tarayya Abuja sun bayyana rashin jin dadi bisa umarnin su yi rajista da hukumar CAC
- Gwamnatin tarayya ce dai ta bayar da umarnin dukkanin masu sana’ar su yi rajista da CAC cikin watanni 2 a kokarin tabbatar da tsaron sana'ar
- Amma wasu na ganin tilasta musu yin rajistar zai kare ne a kan abokan huldarsu da za su karawa kudin hada hada, sannan wasu za su koma ajiya kudi a gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja-Masu sana’ar hada-hadar kudi ta POS a birnin tarayya Abuja sun bayyana bacin rai kan sabon umarnin gwamnatin tarayya na yin rajista da hukumar rajistar kamfanoni ta kasa (CAC).
Gwamnatin tarayya ce dai ta bayar da wa’adin ranar 7 ga Yuli, 2024 ga masu sana’ar hada hadar kudi ta POS, a kan su tabbatar da sun kammala rajista da CAC.
Farashin POS zai iya tashi a Najeriya
A labarin da Vanguard News ta wallafa, wasu daga masu hada-hadar kudi ta POS din sun bayyana cewa matakin zai yi gibi ga ‘yar ribar da suke samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mai sana’ar POS, Kofi Kolawole, ya bayyana cewa dole ne yanzu su karawa abokan huldarsu kudin duk wata hada-hada.
Clement Agbasi, wani mai sana’ar POS a Abuja ya bayyana cewa daukar matakin da gwamnati ta yi zai sa wasu adana kudinsu a gida, kamar yadda The Nation ta tattaro.
“Wasunmu na da rajista,” Kungiyar masu POS
Kungiyar masu hada-hadar kudi ta POS a jihar Kano sta bayyana cewa dama wasu daga cikinsu na da rajista da hukumar CAC.
Kakakin kungiyar, Mukhtar Hashim Adamu ne ya tabbarwa Legit Hausa hakan a yau Laraba, inda ya roki gwamnatin tarayya ta kara wa'adin rufe rajistar.
Mukhtar Hashim Adamu ya kuma nemi a yi hadin gwiwa da kungiyoyin masu sana’ar ta POS domin kammala rajistar cikin sauki.
CBN ya umarci masu POS yin rajista
Mun ruwaito muku a baya cewa gwamnatin tarayya ta umarci masu sana’ar hada-hadar kudi ta POS su yi rajista da hukuma da ke yiwa kamfanoni rajista cikin watanni biyu.
Gwamnati ta bayar da umarnin ne bayan tashi daga tattaunawa da kamfanonin hada-hadar kudi na intanet da shugaban hukumar ta CAC, Hussaini Ishaq Magaji.
Asali: Legit.ng