Dakarun Sojoji Sun Samu Galaba Kan 'Yan Ta'adda Yayin Wani Artabu
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'adɗa masu tayar da ƙayar baya a jihohin Borno da Kaduna bayan sun yi artabu
- A jihar Borno dakarun sojojin sun hallaka wani ɗan ta'adda tare da ceto wani yaro da ƴan ta'adda suka sace a ƙaramar hukunar Nganzai ta jihar
- Dakarun sojojin sun kuma ceto mutum shida tare da ƙwato makamai a hannun ƴan ta'adda bayan an gwabza faɗa a jihar Kaduna
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Dakarun sojojin Najeriya masu yaƙi da ta'addanci a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma sun samu nasara kan ƴan ta'adda a ranar Talata.
Dakarun sojojin sun nuna bajinta inda suka daƙile yunƙurin ƴan ta'adda na yin garkuwa da mutane tare da ceto mutanen da aka yi yunƙurin sacewa.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta fitar a shafinta na manhajar X a ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda
A jihar Borno sojoji sun yi arangama da ƴan ta'addan ISWAP a ƙauyen Kulukawiya da ke ƙaramar hukumar Nganzai ta jihar.
Arangamar ta sanya an sheƙe ɗan ta'adda ɗaya tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya.
Bayanai sun ce sojojin sun kuma ceto wani yaro da ƴan ta'addan suka sace wanda tuni aka sada shi da mahaifinsa, Alhaji Musa.
A wani aikin ceto a jihar Kaduna, dakarun sojoji sun ceto mutum shida da aka sace a ƙauyen Agunu Dutse cikin ƙaramar hukumar Kachia ta jihar.
An ceto mutanen ne ba tare da wani rauni ba kuma tuni aka miƙa su zuwa wajen iyalansu.
Dakarun sojoji sun ƙwato makamai
Hakazalika dakarun sojoji sun yi arangama da ƴan ta'adda a ƙauyen Amale na ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa.
Dakarun sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai sun fatattaki ƴan ta'addan tare da ƙwato makamai a hannunsu.
Makaman da aka ƙwato a hannunsu sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, bindiga ƙirar gida guda ɗaya da adda guda ɗaya.
Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun daƙile wani yunƙurin ƴan ta'adda na yin garkuwa da mutane a jihar Benue.
Dakarun sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai sun ceto wasu mutum biyu da ƴan ta'addan suka yi yunƙurin sacewa a jihar da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng