Kakakin Majalisa Ya Nemi Afuwa Bayan 'Yan Majalisu Sun Kusa Ba Hammata Iska

Kakakin Majalisa Ya Nemi Afuwa Bayan 'Yan Majalisu Sun Kusa Ba Hammata Iska

  • An samu hatsaniya a majalisar dokokin jihar Edo a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu bayan kakakin majalisar ya dakatar da wasu mambobi uku
  • Blessing Agbebaku ya fito ya nemi afuwa a wurin ƴan majalisar bisa wannan hatsaniya da ta ɓarke sakamakon abin da ya aikata
  • Kakakin ya dai dakatar da mambobin ne guda uku bayan ya zarge su da yunƙurin tsige shi tare da sauran shugabannin majalisar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Kakakin majalisar dokokin Edo, Blessing Agbebaku, ya ba da haƙuri kan hatsaniyar da aka samu a majalisar lokacin dakatar da wasu mambobin majalisar a ranar Litinin.

Blessing Agbebaku wanda ke jagorantar majalisar dokokin ya ba da haƙurin ne a ranar Talata, 7 ga watan Mayun 2024, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fusata, ta umurci majalisar dokoki ta tsige gwamna nan take

Kakakin majalisar Edo ya nemi afuwa
Blessing Agbebaku ya nemi afuwa kan rigimar da aka yi a majalisar dokokin jihar Edo Hoto: Rt. Hon. Blessing Agbebaku
Asali: Facebook

Dakatar da 'yan majalisar jihar Edo

Kakakin majalisar a ranar Litinin, 6 ga watan Mayun 2024 ya dakatar da wasu ƴan majalisa uku bisa zarginsu da yunƙurin tsige shi da wasu shugabannin majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan majalisar da aka dakatar su ne Okogbe Donald Okogbe (PDP, Akoko-Edo II), Adheh Isibor (APC, Esan Arewa ta Gabas I), sai Iyamu Bright (PDP, Orhionnwon).

Me kakakin majalisar Edo ya fada?

A kalamansa:

"Ina so na nemi afuwar mambobin wannan majalisa kan abin da ya faru a ranar Litinin a zaman majalisa. Ba nufinmu ba ne mu haifar da tashin hankali a cikin majalisa."
"Mun yi alkawarin hakan ba zai sake faruwa ba. Wannan haƙurin da muka ba da mun bayar ne saboda muna ganin girman ku."

PDP ta ɗauki hanyar sulhu a majalisar Edo

Jaridar Leadership ta ce shugabancin jam’iyyar PDP a jihar ya sanya baki a rikicin da ya kai ga dakatar da ƴan majalisar domin a dawo da su.

Kara karanta wannan

"Da yawa ba su da muƙamai": Jigon APC ya magantu kan zargin rikicin Tinubu da El-Rufai

Wasu daga cikin mambobin sun gana da kakakin majalisar na tsawon sa’o’i a ƙoƙarin ganin an shawo kan rikicin da kuma tabbatar da cewa ƴan majalisar da aka dakatar sun koma majalisar.

Ɗaya daga cikinsu wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce manufar taron ita ce a nemo hanyoyin da za a janye dakatarwar.

A kalamansa:

"Mun haɗu a ranar Talata domin nemo hanyar ɗage dakatarwar da aka yi wa mambobin uku. Za a yi taro a ranar Alhamis kuma da fatan za a ɗage dakatarwar ranar Litinin a zaman majalisa na ranar."

Majalisa ta tsige mataimakin gwamnan Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jjar Edo ta tsige mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, daga muƙaminsa bayan an kammala bincike.

Tsigewar ta biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin bincike na mutum bakwai da majalisar ta kafa domin bincikar zarge-zargen da ake yi wa Shaibu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng