"Yadda Aka Nemi Cin Hanci a Hannun Jami'an Binance a Najeriya"

"Yadda Aka Nemi Cin Hanci a Hannun Jami'an Binance a Najeriya"

  • Shugaban kamfanin kirifto na Binance, Richard Teng, ya yi zargin cewa wasu mutane sun nemi jami'an kamfanin su ba da cin hanci a Najeriya
  • Richard Teng ya bayyana cewa mutanen waɗanda ba a ambaci sunayensu ba, sun nemi a ba su cin hancin domin kawar da zarge-zargen da ake yi wa kamfanin
  • Gwamnatin Najeriya dai ta tsare jami'an kamfanin tare da gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin keta dokokin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Shugaban kamfanin Binance, Richard Teng, ya yi iƙirarin cewa wasu mutanen da ba a san su ba sun nemi cin hancin kirifto daga hannun jami'an kamfanin.

Shugaban na Binance ya ce an nemi cin hancin ne a hannun Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, kafin a tsare su a ranar 28 ga Fabrairun 2024.

Kara karanta wannan

Miyagu sun tafka ɓarna, sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin ruwa a Najeriya

An nemi cin hancin a hannun jami'an Binance
Shugaban Binance ya yi zargin an nemi jami'ansa su ba da cin hanci a Najeriya Hoto: @_RichardTeng, @binance
Asali: Twitter

Shugaban Binance ya yi rubutu

Shugaban na Binance yayi wannan iƙirarin ne a wani rubutu a shafin yanar gizo na kamfanin Binance.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ributun ya yi cikakken bayani kan yadda jami'an Binance suka yi ƙoƙarin tattaunawa da hukumomin Najeriya, ciki har da taron da suka yi a Abuja ranar 8 ga watan Janairu, kafin a zarge su da aikata laifuka.

A cewarsa, an shirya taron ne da gwamnatin Najeriya ta hanyar wani kwamiti da ya ƙunshi kusan hukumomi 30.

Zargin kamfanin Binance kan Najeriya

Wani ɓangare na rubutun na cewa:

"Taron ya ƙare inda shugaban kwamitin ya ba da tabbacin cewa za su duba lamarin sannan su tuntuɓi lauyoyin mu."
"Sai dai, a lokacin da jami'an mu ke barin wurin taron, wasu mutane da ba a sansu ba sun tuntuɓe su tare da ba su shawarar su biya kuɗaɗe domin a kawar da zarge-zargen."

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida ya kaddamar da titi mai hawa 3 a kan kudi ₦15bn a Dan Agundi

"Lauyoyin mu sun sanar mana da cewa an ba su zaɓin a biya wasu kuɗaɗe cikin kirifto a sirrance cikin sa'o'i 48 domin a kawar da zarge-zargen, sannan ana buƙatar sanin matsayar mu da safe."

Richard Teng ya bayyana cewa ba su karɓi wannan tayin na ba da cin hanci ba.

Jami'in Binance ya tsere daga Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaya daga cikin shugabannin kamfanin Binance da aka tsare a birnin Abuja, Nadeem Anjarwalla ya tsere.

Matashin ya tsere ne bayan jami’an tsaron da ke kula da shi sun ba shi damar zuwa masallaci da ke kusa domin gudanar da ibada saboda watan azumi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng