Tinubu Yana Kasar Waje Saboda Rashin Lafiya? Minista Ya Fadi Gaskiya

Tinubu Yana Kasar Waje Saboda Rashin Lafiya? Minista Ya Fadi Gaskiya

  • Gwamnatin tarayya ta fito ta yi magana kan batun jita-jitar rashin lafiyar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ake yaɗawa
  • Ƙaramin ministan lafiya da walwalar jama'a, Dr. Tunji Alausa ya kwantar da hankulan ƴan Najeriya inda ya ce lafiyar Tinubu ƙalau
  • Ministan ya kuma bayyana cewa shugaban ƙasan a wasu lokutan a cikin gida Najeriya ake duba shi dangane da rashin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ƙaryata raɗe-raɗin da ake ta yaɗawa dangane da rashin dawowar shugaban ƙasa Bola Tinubu gida Najeriya.

Gwamnatin tarayyar ta bayyana cewar lafiya ƙalau shugaba Bola Tinubu yake saɓanin jita-jitar da ake yadawa cewa ya je neman lafiya ne.

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana lokacin dawowar Tinubu gida Najeriya

Tinubu na cikin koshin lafiya
Gwamnati ta ce Bola Tinubu yana cikin koshin lafiya a Turai Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Karamin ministan lafiya da walwalar jama’a, Dr. Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels tv a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu dai har yanzu bai dawo Najeriya ba kwanaki bayan kammala taron tattalin arziƙi na duniya da aka gudanar a ƙasar Saudiyya, lamarin da ya jawo cece-kuce kan inda ya tafi.

Tinubu ya je neman magani?

Sai dai, Tunji Alausa yayin da yake mayar da martani kan jita-jitar, ya ce Tinubu ba neman magani ya tafi ba ƙasar waje.

"Bari na gaya muku, muna samar da tsarin kiwon lafiya ga ƴan Najeriya ba shugaban ƙasa kaɗai ba. Muna da ƴan Najeriya miliyan 220 wannan shi ne abin da shugaban ƙasa yake so."
"Muna da shugaban ƙasa wanda yake da lafiya, mai ƙoshin lafiya sannan yana jagorantar ƙasar nan ta hanyar da ta dace."

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan Nuhu Ribadu ya yi babban rashi a rayuwarsa

"Shugaban ƙasa yana samun wani ɓangare na kula da lafiyarsa a Najeriya."

- Dr. Tunji Alausa

Ku kalli bidiyon a nan:

Lokacin dawowar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta bayyana lokacin dawowar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu daga ƙasar waje.

Bayo Onanuga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya a ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng