Daga Karshe an Bayyana Lokacin Dawowar Tinubu Gida Najeriya
- Fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida Najeriya a ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2024
- Shugaban ƙasan dai ya kwashe kwanaki ba shi a cikin ƙasar nan bayan ya halarci wani taro a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya
- Hakan ya jawo cece-kuce inda wasu ke tunanin cewa ko ya wuce birnin Paris ne domin a duba lafiyarsa a can
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa a ranar Talata, 7 ga watan Mayu, ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai dawo Najeriya ranar Laraba, 8 ga watan Mayu daga nahiyar Turai.
A cewar Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya tare da hadimansa.
Bayo Onanuga ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na manhajar X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da hadimansa za su dawo Najeriya gobe daga nahiyar Turai."
- Bayo Onanuga
Kwanaki nawa Tinubu ya yi a waje?
Ranar Talata, 7 ga watan Mayu, ta yi daidai da cikar kwanaki takwas bayan Tinubu ya halarci taron tattalin arziƙi na duniya a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.
Sai dai, har yanzu shugaban ƙasan bai dawo Najeriya ba tun bayan kammala taron.
Taron na kwanaki biyu, an buɗe shi ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Afrilu, kuma ya kare a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu, 2024.
Ba a ji ɗuriyar shugaba Tinubu ba
Fadar shugaban ƙasar dai ba ta fitar da wata sanarwa kan abin da ya hana shugaban ƙasan dawowa gida Najeriya ba.
Hakan ya haifar da cece-ku-ce a wasu ɓangarori inda har wasu ke cewa mai yiwuwa Shugaba Tinubu ya zarce zuwa birnin Faris na ƙasar Faransa, inda a baya ya je aka duba lafiyarsa.
Mataimakin Tinubu, Kashim Shettima, ya shirya zuwa Amurka domin wakiltar shugaban ƙasan a wajen wani taro.
Idan za a tuna, amma ba zato ba tsammani ya soke tafiyar, inda ya dora alhakin hakan kan matsalar da jirgin saman ya samu.
SERAP tana shirin kai Tinubu kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya janye maganar saka harajin 0.5% ga abokan hulɗar bankuna.
Ƙungiyar SERAP ta bayyana cewa lauyanta, Ebun-Olu Adegboruwa a shirye yake tsaf domin shigar da larar gwamnatin idan ta ƙi janye dokar.
Asali: Legit.ng