'Yan Ta'adda Sun Hallaka Mutum 2 da Sace Wasu da Dama a Kaduna
- Ƴan ta'adda sun kai wani sabon hari a ƙaramar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Ƴan ta'addan ɗauke da makamai a yayin harin sun hallaka mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum 18 da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
- Mutanen ƙauyen da lamarin sun koka da yawan hare-haren da ƴan ta'adda suke kai musu inda suka buƙaci gwamnati da ta kawo musu ɗauki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Ƴan ta'adda sun hallaka mutum biyu tare da yin garkuwa da mutum 18 a Unguwan Dantata da ke ƙauyen Gefe na gundumar Kallah a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Ƴan ta’addan sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Litinin, ga watan Mayun 2024.
Wani mazaunin ƙauyen mai Sujada Ayuba, shi ne ya tabbatarwa jaridar The Punch aukuwar lamarin a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan ta'adda sun addabi ƙauƴen Kaduna
Ya bayyana cewa tun a watan Nuwamban shekarar da ta gabata ƴan ta’adda ke damun al’ummar yankin Gefe, wanda hakan ya sanya sun kashe kuɗaɗe masu yawa wajen biyan kuɗin fansa.
"Wannan ƙauyen yana buƙatar taimakon gwamnati sannan babban abin da suke yi shi ne noma. Yanzu an shigo damina sannan mafi yawa daga cikinsu ba za su iya gonakinsu ba saboda tsoron kada a sace su.
"Duk sun siyar da abin da suka noma wasu har da gonakinsu domin su haɗa kuɗin fansan ƴan uwansu da aka sace.
Muna buƙatar taimakon gwamnati kamar abinci da taki domin rage raɗaɗin yunwar da ake fama da ita a ƙauyenmu."
- Sujada Ayuba
An birne wadanda 'yan ta'adda suka kashe
Ya bayyana cewa har yanzu ƴan ta'addan ba su kira waya ba domin cinikin kuɗin fansan da za a biya su, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Ya ƙara da cewa mutum biyun da aka kashe an binne su a yau Talata, 7 ga watan Mayu kamar yadda addinin Kiristanci ya tanada.
Ko da Legit Hausa ta tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, bai amsa kiran waya da saƙon da aka tura masa ba.
Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun hallaka mutum shida tare a wani hari da suka kai a ƙauyen Ambe da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna.
Miyagun ƴan bindigan waɗanda suka ɗauke da muggan makamai sun kuma raunata wasu mutum takwas a harin ta'addancin da suka kai a ƙauyen.
Asali: Legit.ng