Maganin gargajiya na kasar Madagascar ba ya warkar da cutar korona - WHO

Maganin gargajiya na kasar Madagascar ba ya warkar da cutar korona - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta na nan dai a kan bakanta na cewa kawo yanzu ba a samu wani maganin cutar korona ba, saboda haka mutane su daina amfani da maganin da ba shi da tabbas.

Hakan ya sanya WHO ta yi watsi da ikirarin da shugaban Madagascar ya yi na cewa maganin gargajiya da aka samar a kasarsa na iya warkar da masu cutar sarkewar numfashi ta korona.

Kasar Madagascar dai wani tsibiri ne a tsakiyar tekun Indiya da ke da nisan kilomita 400 daga gabashin Afirka, al’ummar kasar sun kai miliyan 26 tun kidayar da aka gudanar a shekarar 2018.

Sai dai duk da wannan gargadi na Hukumar Lafiya ta Duniya, wasu kasashen Afirka kamar su Tanzania da Guinea-BIssau, sun daura damarar kammala duk wani shiri na shigo da maganin na Madagascar.

Kasashen baya ga bayyana farin cikinsu da kuma alfahari da kasar Madagascar, sun yi amanna da yadda maganin ke yakar cutar korona.

Madagascar ta binciko wannan magani na gargajiya daga wani ganye wanda ta sarrafa shi kamar ganyen shayi, kuma ta sanya masa suna COVID-Organics.

Covid-Organics Hakkin mallakar hoto: Aljazeera

Covid-Organics Hakkin mallakar hoto: Aljazeera
Source: Twitter

A ranar Litinin, 20 ga watan Afrilun 2020, shugaban kasa Andry Rajoelina ya kaddamar da maganin, wanda suke amfani da shi wajen magance cutar Coronavirus.

Maganin COVID-Organics ya warkar da mutane 92 daga cikin mutane 128 da suka kamu da cutar a kasar, 36 suka rage, kuma ba’a samu mutum daya da ya mutu sakamakon cutar ba.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Gwamnatin Tarayya ta yi kira da a fara bincike domin neman maganin gida

A zahiri dai wannan magani yana dauke da sunadarin artemisia, wanda akasari ake amfani da shi don maganin zazzabin cizon sauro, kuma Cibiyar bincike ta ta kasar ita ce ta binciko maganin.

Duk da tasirin wannan maganin a kasar Madagascar na warkar da masu cutar korona, Hukumar Lafiyar na ci gaba da jaddada cewa, maganin bai samu tabbacin masana kimiyya ba saboda haka bai inganta ba.

Sai dai ko shakka babu, wannan ra'ayi ya sha ban-ban da shugaban Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo da takwaransa na Tanzania, John Magufuli, inda tuni suka bazama wajen shigo da maganin kasashensu.

Shugabannin biyu sun ce lallai al'ummominsu za su ribaci wannan magani domin magance cutar korona wadda ta zamto alakakai a fadin duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel