Kanun Jaridu: Gwamnati Za Ta Yi Wa Mutane Miliyan 1.9 Rajistar Sana’ar PoS
Rahotannin da ke nuna yadda aka dakile hanyoyin kasuwanci na cryptocurrency domin karfafa darajar Naira, da kuma cajar 0.5% na harajin tsaron yanar gizo ga abokan huldar bankuna, suka mamaye shafukan farko na jaridun Najeriya.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A yau Talata, 7 ga watan Mayu, 2024, Legit Hausa ta yi duba kan manyan kanun labaran da jaridun kasar nan suka buga.
An tsamo labaran ne daga shafukan farko na jaridun wadanda ake kyautata zaton sun fi jan hankalin masu karatu a yau, kamar yadda jaridar The Cable ta tattara.
Kanun labaran manyan jaridun Najeriya
1. Jaridar The Punch
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta shirya cire Naira daga duk wata manhaja ta Crypto, a daidai lokacin da take kokari wajen farfado da darajar Naira.
Jaridar ta ce 'yan Najeriya sun ki amincewa da rage kudin wutar da aka yi ga abokan ciniki na rukunin 'Band A' daga N225/kWh zuwa N206.8/kWh.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin yin rajistar masu sana'ar PoS mutum miliyan 1.9.
2. Jaridar Daily Trust
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta ce babu wani shiri na kafa sansanin soji na kasashen waje a Najeriya.
Jaridar ta ce Yakubu Gowon, tsohon shugaban kasa, ya ce da Najeriya ta kasance kasa mafi inganci idan da tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua ya kammala wa’adinsa.
3. Jaridar The Guardian
Jaridar The Guardian ta rawaito cewa har yanzu ba a san inda shugaban kasa Bola Tinubu yake ba yayin da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Amurka saboda tangardar jirgi.
Jaridar ta ce Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ba da umarnin takaita kai wuta ga abokan hulda da ke a wasu kasashe.
4. Jaridar THISDAY
Jaridar THISDAY ta rawaito cewa fadar shugaban kasa ta caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kan sukar Tinubu da dansa Seyi.
Tinubu ya yi zargin cewa akwai alaka tsakanin Seyi da kamfanin Chagoury wanda zai haifar da rikici a kwangilar da gwamnati ta bayar.
Jaridar ta ce Babban bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da su fara karbar harajin 0.5% domin turawa 'asusun tsaron yanar gizo.'
Biyan harajin saka kudi a banki
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito Babban bankin Najeriya (CBN) ya ba bankuna umarnin dawo da dokar cajar harajin 2% a duk lokacin da abokan hulda za su saka kudi a bankunan.
Wannan dai na zuwa ne watanni akalla hudu bayan da babban bankin ya dakatar da dokar a watan Disambar 2023 tare da kayyade wa'adinta zuwa karshen watan Afrilu, 2024.
Asali: Legit.ng