Gwamnatin Tarayya Ta Kuma Juyowa Kan 'Yan Kirifto Domin Inganta Naira a Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Kuma Juyowa Kan 'Yan Kirifto Domin Inganta Naira a Najeriya

  • Gwamnatin Tarayya ta sake juyowa ta kan 'yan Kirifto a Najeriya domin tabbatar da dakile kasuwanci ba bisa ka'ida ba
  • Hukumar SEC a Najeriya ta tabbatar da hakan inda ta ce za ta dauki tsauraran matakai domin inganta darajar Naira a kasar
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin kasuwancin 'yan Kirifto na kawo cikas da daidaituwar farashin Naira a kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar SEC ta shirya daukar mataki kan masu kasuwancin Kirifto ba bisa ka'ida ba a Najeriya.

Hukumar ta shirya daukar matakin ne domin tabbatar da ingancin kasuwanci da kare muradun masu hannun jari.

Gwamnati za ta dakile masu Kiripto ba bisa ka'ida ba domin daga darajar Naira
Gwamnatin Tarayya ta shirya ɗaukar mataki kan masu kasuwancin Kiripto ba bisa ka'ida ba domin farfaɗo da Naira. Hoto: Presidency.
Asali: Getty Images

Matsalolin Kirifto kan darajar Naira

Kara karanta wannan

Kanun jaridu: Gwamnati za ta yi wa mutane miliyan 1.9 rajistar sana'ar PoS

Daily Trust ta tattaro cewa wannan bai rasa nasaba da koma baya da harkar ke jawowa Naira a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karyewar darajar Naira ya saka bankin CBN daukar wasu matakai domin inganta farashinta a kasuwa, cewar BusinessDay.

Mukaddashin babban darektan Hukumar, Dakta Emomotimi Agama shi ya bayyana haka inda ya ce za su dauki tsauraran matakai kan lamarin.

Agama ya bayyana haka ne yayin taron kungiyar 'yan Kiripto a Najeriya (BICCoN) inda ya ce za su daidaita farashin Naira.

Zargin illar hada-hadar Kirifto ga Naira

Ana zargin 'yan Kiripto suna kawo matsala game da farashin Naira yayin da suke amfani da dala a harkokin kasuwancinsu.

Hakan ya jefa Naira a cikin wani hali wanda ya shafi farashin kayayyakin abinci a ƙasar da sauran kayan masarufi.

A watan Janairun wannan shekara, Gwamnatin Tarayya ta dakatar da amfani da mahajojin Kiripto kamar su Binance da OctaFX da sauransu.

Kara karanta wannan

Hukumar UBEC za ta yi horo na musamman ga malamai 1480

An fara samun saukin farashin abinci

A wani labarin, mun ruwaito muku cewa an fara samun saukin farashin kayayyakin abinci a wasu jihohin Arewacin Najeriya.

Dillalan kayan abinci a jihohin Bauchi da Gombe da kuma Jigawa sun tabbatar da cewa farashin ya fara sauka a wurarensu bayan tashin gwauron zabi.

'Yan kasuwar sun tabbatar da cewa hakan bai rasa nasaba da matakan da Gwamnatin Tarayya ke dauka na dakile masu boye kayan abinci da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.