Bankuna Sun Dawo Cire Kaso 2% Idan Abokan Hulda Za Su Ajiye Sama da N500,000
- Bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi sun dawo da karbar haraji kan kudaden da abokan hulda ke sakawa a asusun bankunan
- Wannan na zuwa ne bayan da CBN ya dakatar da karbar harajin saka kudin da suka haura N500,000 a banki a watan Disambar 2023
- Bankuna yanzu za su caji kaso 2% ga kudin ajiyar da suka haura N500,000 da kuma kaso 3% ga kudin da ajiyar da suka haura N3,000,000"
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sake dawo da karbar haraji kan kudaden ajiya da suka haura N500,000 ga daidaikun mutane da kuma kamfanoni.
Watanni hudu da suka gabata ne babban bankin ya dakatar da karbar harajin saka kudin da suka haura N500,000 a banki har zuwa ranar 30 ga Afrilu, 2024.
Haraji kan ajiye N500,000 a banki
A wata sanarwa da aka rabawa abokan hulda, bankin First Bank Nigeria (FBN) ya ce an dawo karbar harajin ne daga a ranar 1 ga watan Mayu, jaridar The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga daidaikun mutanen da ke saka sama da N500,000, banki zai caji kaso 2% na adadin da za a saka.
Hakazalika, ga kamfanoni, duk mai son saka sama da N3,000,000, to tabbas zai ba da kaso 3% na adadin da zai saka.
Bankuna sun aikawa abokan hulda sako
A cewar rahoton jaridar Thisday, bankuna sun kuma aike da sakwannin imel ga abokan huldar su inda suka sanar da ci gaba da karbar harajin.
"Muna sanar da ku cewa, daga ranar 1 ga Mayu 2024, an daidaita kudin da ake caja yayin saka kuɗi kamar yadda hukuma ta bukata.
"Saboda haka, za a dawo da amfani da cajar kudin kamar haka: Kaso 2% ga kudin da suka haura N500,000 da kuma kaso 3% ga kudin da suka haura N3,000,000."
- Sanarwar bankin FBN.
CBN ya kawo harajin tsaron yanar gizo
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa Babban Bankin Najeriya a ranar Litinin ya umurci bankuna da su fara cajar kaso 0.5% na harajin tsaron yanar gizo kan hada-hadar kudaden abokan hulda.
Wata takardar sanarwa da babban bankin ya fitar a ranar Litinin ta ce za a fara fara aiwatar da karbar harajin nan da makonni biyu.
Asali: Legit.ng