Hukumar UBEC Za Tayi Horo Na Musamman Ga Malamai 1480

Hukumar UBEC Za Tayi Horo Na Musamman Ga Malamai 1480

  • Hukumar ilimin bai daya ta kasa (UBEC) ta kaddamar da shirin horar da malamai 1,480 daga karkara a fadin Najeriya
  • Sakataren hukumar, Dakta Hamid Bobboyi ya ce horon za a yi shi ne domin farfaɗo da darajar harkar ilimi da ilmantarwa
  • Legit ta tattauna da wani malamin karkara, Yusuf Saidu Danbakwai, domin jin yadda za su yi fatan cin gajiyar shirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa (UBEC) ta kaddamar da shirin horar da malamai 1480 a fadin Najeriya.

Teachers in class
Hukumar UBEC za ta horar da malamai domin bunkasa ilimi. Hoto: Olukayode Jaiyeola/Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Rahoton da jaridar Tribune Online ta fitar ya nuna cewa shirin zai karkata ne wajen yin horo na musamman kan dabarun koyarwa.

Kara karanta wannan

Kakakin majalisar jihar Niger zai aurar da marayu 100

Horon zai mayar da hankali ne kan malamai da suke karkara da kuma lunguna domin bunkasa ilimin yankunan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adadin malaman da za a dauka

Ana sa ran malami 40 ne daga kowace jiha da birnin tarayya za a zaba domin cin gajiyar shirin, cewar jaridar Daily Post.

Daga cikin kyakkyawan zaton da ake shine idan shirin ya samu nasara zai kawo canji a harkar koyarwa a karkara.

Jawabin sakataren UBEC na kasa

Sakataren hukumar UBEC, Dr. Hamid Bobboyi, ya bayyana cewa daga cikin kalubalen da suke fuskanta shine rashin samun ingantaccen ilimi ga dalibai da suke karkara.

Shugaban yana cewa lallai a kauyuka da lunguna ana wahalar samun kwararrun malamai da za su rika bada ilimi yadda ya kamata.

Ta kuma kara da cewa hakan na taimakawa wajen rashin samun wadatattun dalibai a makarantu, wasu iyayen ma suna cire yaransu daga makarantun saboda matsalar.

Kara karanta wannan

Kudurin Majalisa: Za a rika yankewa masu safarar miyagun kwayoyi hukuncin kisa

Fa'idar da horon malaman zai haifar

A wani jami'in hukumar ta UBEC, Mista Mayowa Aleshin ya ce wannan kokarin da hukumar ke yi ya nuna cewa gwamnati tana kokarin inganta ilimi.

Ya kuma bayyana cewa wannan kokarin ana yinsa ne domin tabbatar da kowane dan Najeriya ya samu ilimi ingantacce.

Wurin yaki da matsalar yaran da ba su zuwa makaranta kuwa, mista Aleshin ya ce wannan itace babbar hanya domin matsalar yawanci daga karkara ta ke.

Jawabi daga malamin karkara

Wani malamin makaranta da ke garin Kuri da ke karamar hukumar Yamaltu Deba a jihar Gombe, Yusuf Saidu Danbakwai yace shirin zai bada fa'ida matukar aka yi shi da gaske.

Sai dai ya ce adadin malaman da UBEC za ta dauka ba lallai ya biya bukata ba. A cewarsa, idan ana son samun fa'ida cikakkiya dole a kara adadin ko kuma a rika daukan malamai akai-akai ana musu horo.

An yi kira ga Tinubu kan Ilimi

Kara karanta wannan

Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari

A wani rahoton, kun ji cewa an yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya ba da umurnin janye batun karin kudin jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) domin a bunkasa ilimi.

Wakilin Daliban Durbin Katsina, Sanusi Yau Mani ne ya yi wannan kiran a zantawarsa da Legit Hausa inda ya ce ya kamata ilimi ya zama kyauta a Najeriya idan ana son magance ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng