Katsina: Masari ya dauka malaman makaranta 4,250 don inganta ilimi

Katsina: Masari ya dauka malaman makaranta 4,250 don inganta ilimi

- Gwamnatin jihar Katsina ta dage wurin bunkasa harkokin ilimi a jihar

- Gwamnatin jihar ta horar da a kalla malamai 4,250, daga 2015 zuwa yanzu

- Sannan an gyara makarantun sakandare da na firamare a fadin jihar

A kalla malaman makarantun firamare da na sakandare 4,250 gwamnatin jihar Katsina ta horar tsakanin 2015 zuwa yanzu.

Duk da haka, S-Power tana kara horar da malamai 7,000 don bunkasa ilimi a jihar, Channels Tv ta wallafa.

Gwamna Aminu Masari ya sanar da hakan a wani taro na bunkasa ilimi a jihar Katsina na 2020, wanda aka yi a ofishin kananan hukumomi da ke Katsina.

Katsina: Masari ya dauka malaman makaranta 4,250 don inganta ilimi
Katsina: Masari ya dauka malaman makaranta 4,250 don inganta ilimi. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

Gwamnan, wanda shine babban bako, ya samu wakilcin mataimakinshi, Mannir Yakubu, wanda ya gabatar da jawabi mai taken 'Nisan tafiyarmu'.

Yakubu ya bayyana cigaban da gwamnatin ta samar tun daga 2015 zuwa yanzu, musamman a kan harkokin ilimi.

A cewarsa, an yi gine-gine, daukar sababbin malamai, bunkasa makarantu, samar da kayan koyo da koyarwa, da kuma samar da abubuwan zamani a makarantu.

Ya ce gwamnatin jihar ta gyara azuzuwa 2,294, ofisoshi 1,334 da ma'adanai, sun bunkasa makarantun firamare 12 har da mayar da su benaye.

KU KARANTA: Mata ta tana lalata da fastonmu da kuma dattawan cocinmu, Magidanci

Baya ga haka, ta haka burtsatsai 70 a wasu makarantun firamare, bandakuna 930 a makarantu da dama don inganta lafiyar dalibai da malamai.

"An gina kuma an gyara makarantun sakandare da ke fadin jihar. Sannan an gyara makarantun sakandare 38 an dan yi gyaran sama-sama a makarantu 37, saboda lalacewar da suka yi," a cewarsa.

Sannan hatta makarantun jami'o'i ba a bar su a baya ba, an gyara sashin ilimin noma da kiwo a jami'ar Umar Musa Yar'Adua kuma ana gina katangar masallaci.

KU KARANTA: Soji sun kashe mayakan Boko Haram 23, sun cafke kwararren mai hada bam

Sannan ana gina wurin kwanan dalibai mata da sashin gwaje-gwaje a kwalejin koyon koyarwa ta Isah Kaita da ke Dutsinma. Sannan an kara da gyaran tituna da wurin kwanan dalibai na kwalejin Dr Yusufu Bala Usman da ke Daura.

Sannan ya bayyana yadda gwamnatin ta mayar da hankalinta wurin biyan WAEC, NECO, NABTEB da kuma NBAIS, da kuma daukar nauyin 'yan jihar Katsina su tafi kasashen ketare don karatu a fannoni daban-daban.

A wani labari na daban, hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani dan sanda Basiru a wuraren Rumawa da ke karamar hukumar Ungogo a kan laifin lalata.

Kamar yadda hukumar tace, an kama har da Basiru abokin Jamilu a wani daki da ke wuraren Rumawa, inda suka boye suna aikata alfashar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel