Sarkin kano: Rashin Ilimi ke jawo fitinu a Arewacin Nigeria

Sarkin kano: Rashin Ilimi ke jawo fitinu a Arewacin Nigeria

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kalubalanci shuwagabannin Arewa dasu chanza yanayin gudanar da harkar Ilimi a yankin domin cigaban kasa.

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari, wanda Jihar shi take fama da rikicin yan bindiga da garkuwa da mutane yace samar da ilimi shine mafitar kashe –kashe da ta’addanci.

Shugaban Majalissar dattawa, Ahmad Lawan yayi kira akan bunkasa ilimi a arewa, yace rashin zuwan yara makaranta akalla kimanin miliyan 14 babbar matasala ce.

Sarkin kano da Shugaban Majalissar dattawa sun bayyana hakane a kaduna shi kuma masari ya bayyana hakane yayin da tawagar Shugaban kasa suka kaima ta’aziya a katsina ranar Litinin.

Sarkin kano: Rashin Ilimi ke jawo fitinu a Arewacin Nigeria
Sarkin kano: Rashin Ilimi ke jawo fitinu a Arewacin Nigeria
Asali: Facebook

KU KARANTA An dage zaman sake duba shariar Imo zuwa watan gobe

Sarkin kano ya kara da cewa arewa cin kasar zata gurbatar da kanta, Idan bata yi yaki da talauci, rashin ilimi, miyagun kwayoyi, cutar tamowa, da matsalolin boko haram ba.

Ya kara da cewa babu wani Shugaban Arewa da zai yi farin cikin kalubalen dake fuskantar kasar.

Yace kashi tamanin da bakwai cikin dari na talaucin Nigeria yana Arewa da miliyoyin yara ba ilimi.

“Akwai matsalolin almajirai, miyagun kwayoyi da na boko haram cike a arewa.” A cewarsa

Yace Jihohi tara daga arewa sun dau kashi hamsin cikin dari na cutar tamowa.

Ya bukaci shuwagabanni Yankokin dasu samar da Ilimi, asibitoci da abinci mai gina jiki hakan zaisa a kawar da tashin hankali da fitittinu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng