'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyen Kaduna, Sun Kashe Mutane da Dama
- Akalla mutane shida ne suka mutu yayin da wasu takwas suka samu raunuka a wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Kaduna
- Daniel Amos, 'dan majalisa wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a majalisar wakilai, ya ce an kai harin ne a kauyen Ambe da ke Sanga
- Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna Mansir Hassan wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an kama dan bindiga daya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum shida tare da raunata wasu 8 a wani hari da suka kai a kauyen Ambe da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna.
An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti bayan faruwar lamarin, jaridar The Cable ta ruwaito.
Dan majalisar Jema’a/Sanga ya magantu
Daniel Amos mai wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a majalisar wakilai, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan majalisar ya nuna bakin cikinsa kan lamarin, ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kamo wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Ya yi kira ga daukacin al’ummar karamar hukumar Sanga da su kwantar da hankalinsu a yayin da suke kokarin ganin an kawo karshen matsalar rashin tsaro a yankin.
"An kama dan bindiga" - Hassan
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna Mansir Hassan ya yi magana kan lamarin ga gidan talabijin na Channels, inda ya ce an kama mutum daya da ake zargi da kai harin.
A cewar Hassan, jami’an ‘yan sanda daga ofishin ‘yan sanda reshen Sanga da kuma dakarun sojoji na ‘Operation Safe Haven’ suka garzaya garin domin kai dauki bayan samun kira.
Ya ce jami'an tsaron sun yi musayar wuta da 'yan ta'addan inda aka kama daya daga ciki yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji.
Sojojin Nijar sun kama Kachallah Mai Daji
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa sojojin Jamhuriyar Nijar sun kama Kachallah Mai Daji, wani rikakken shugaban 'yan bindiga na Najeriya.
An tattaro sojojin Nijar sun kama Kachallah Mai Daji a lokacin da yake kokarin satar dabbobi a yankin Illela da ke kan iyakar Najeriya da Nijar.
Asali: Legit.ng