Abba Gida Gida ya Kaddamar da Titi Mai Hawa 3 kan Kudi ₦15bn a Dan Agundi
- Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da ginin titin sama a kan ₦15bn a titin 'Dan Agundi domin rage cunkoson abubuwan hawa a yankin
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya kaddamar da titin mai hawa uku a ranar Lahadin nan domin ganin yadda za a fara gudanar da aikin
- An ba kamfanin CCG Nigeria Limited aikin kuma ana sa ran zai kammala kwangilar titin zamanin a cikin watanni goma sha takwas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya dora tubalin ginin titin saman da kudinsa ya kai Naira Biliyan 15 a wuraren Kofar 'Dan Agundi a kwaryar birnin Kano.
Gwamnati ta bawa kamfanin CCG Nigeria Limited kwangilar aikin da ake sa ran kammalawa cikin watanni goma sha takwas domin rage cunkoson ababen hawa a yankunan.
A sakon da Sanusi Bature Dawakin Tofa, darakta janar na gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook, kammala titin zai kawo ci gaba a jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Za a gama aikin da wuri," Wang
Yayin kaddamar da aikin titin mai hawa uku, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa na ayyukan raya kasa a fatansa na mayar da Kano babban birni.
Ya ce ya bayar da wasu kwangilolin manya-manyan titunan a Tal'udu a kokarin rage cunkoso, kamar yadda Channels Television ta wallafa.
"Mun samar da wasu hanyoyin da masu ababen hawa za su bi a kokarin bin dokokin aikin da kuma tsare masu amfani da titunan."
A jawabinsa, Manajan ayyuka a kamfanin CCG Nigeria Limited, Mista Gee Wang ya yi alkawarin kammala aikin cikin watanni sha takwas din aka tsara tun da fari.
Za a gina titin Kano a watanni 4
Mun ruwaito muku cewa gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar gina Western bypass ga kamfanin Dantata and Sawoe, inda gwamnatin ta yi gargadin a kammala aikin da wuri.
Ministan Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Umar Ibrahim El-Yakub ya ce za a kammala aikin cikin watanni hudu saboda an samar da dukkanin abubuwan da ake bukata wajen gudanar da aikin.
Asali: Legit.ng