Sabani Ya Barke Tsakanin ’Yan Awaren Biafra da Ke Fafutukar a Tsaga Najeriya Gida 2
- ‘Yan fafutukar kafa kasar Biafra sun samu sabani kan yadda za su tirsasawa Inyamurai zaman gida a cikin ‘yan kwanakin nan
- Rahoto ya naqalto yadda shugabannin tafiyar ke sanya ranaku mabambanta, lamarin da ke hango kura a hadin kan ‘yan awaren
- Gwamnatin Najeriya ta sha alanta haramta Biafra da masu fafutukar kafa ta, lamarin da ke daukar salo a kowanne lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Najeriya - Gwamnatin Jamhuriyar Biafra ta ‘yan gudun hijira (BRGIE), ta samu sabani da abokiyarta ta ’yan asalin yankin Biafra (IPOB) kan ranar da za su tirsasa zaman gida don karrama jaruman Biafra da suka mutu a Yakin Basasan 1967-1970 a Najeriya.
A wata sanarwa da Firayim Ministan BRGIE, Simon Ekpa ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa zaman gida a yankin Biafra ya fara ne daga ranar 29 zuwa 31 ga Mayu 2024.
Idan baku manta ba, ita kuwa IPOB ta alanta ranar da za ta tirsasa zaman gida a yakin ne a matsayin 30 ga watan Mayun 2024, rahoton Jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin tirsasa zaman gida ga Inyamurai daga BRGIE
Sai dai kuma firaministan BRGIE, Ekpa ya ce zaman gida zai dauki tsawon kwanaki uku ne kuma ya zama dole domin baiwa ‘yan Biafra damar kada kuri’ar ‘yan kasarsu, rahoton Daily Post.
Ekpa wanda ya bayyana cewa ba shi da daraja a mutunta zaman gida ba tare da ‘yan kabilar Igbo sun kada kuri’unsu don ‘Yancin Biafra ba, ya ce yakin basasar Biafra ya kare ne a kafafen yada labarai kawai, amma har yau gwamnatin Najeriya na yaki da ‘yan Biafra.
Ya kuma bayyana cewa, zaman gidan ba zai yi amfani ba matukar Inyamurai basu samu damar kada kuri’arsu ta ‘yanci ba, inda yace ririta yakin basasar Biafra ta kare ne a kafafen yada labarai.
Gwamnatin Najeriya na cigaba da yakar Biafra, BRGIE
Hakazalika, ya ce yakin basasar bata kare ba, domin har yanzu gwamnatin Najeriya na ci gaba da yakar ‘yan Biafra.
Ya zuwa yanzu, shugaban IPOB Nnmadi Kanu na cigaba da zama a hannun gwamnatin Najeriya, inda yake jiran shari’a kan tuhume-tuhume da dama.
Gwamnatin Najeriya ta sha alanta ‘yan fafutukar kafa kasar Biafra a matsayin ‘yan ta’adda, duba da yadda suke barna a Kudancin Najeriya.
Jita-jita kan Tinubu ya amince a raba Najeriya
A wani labarin, mun binciko maku gaskiya kan wata jita-jita da aka yada cewa, gwamnatin Tinubu ta amince a raba Najeriya.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da 'yan aware ke bayyana aniyarsu na dole a raba kasar kowa ya kwashi gadonsa.
Sai dai, bincike ya nuna cewa, babu wani batu daga fadar shugaban kasa da ke tabbatar da an yi maganar rabon kasa.
Asali: Legit.ng