EFCC Na Tuhumar Wasu Tsofaffin Gwamnoni 58 Kan Badakalar N2.1tn? Gaskiya Ta Fito
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta yi magana kan rahoton da ya ce ta fitar da sunayen tsofaffin gwamnonin da ake tuhumarsu
- A ranar Asabar ne wasu kafofin watsa labarai suka fitar da rahoton cewa tsofaffin gwamnoni 58 na fuskantar tuhukuma kan wawure N2.187tn
- Sai dai a wata sanarwa, kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana wannan rahotan a matsayin 'labarin karya da yaudara'
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar EFCC, ta musanta rahoton da ke cewa ta fitar da jerin sunayen tsofaffin gwamnonin da ake bincike kan zargin almundahana.
Hukumar na martani ne kan wani rahoto mai taken: “EFCC ta saki cikakken jerin sunayen tsofaffin gwamnoni 58 da suka wawure Naira Tiriliyan 2.187,” in ji rahoton Channels TV.
Rahoton da EFCC ke magana a kansa
A ranar Asabar ne wasu kafofin watsa labarai suka fitar da rahoton cewa tsofaffin gwamnoni 58 na fuskantar tuhukuma daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa hukumar na zargin tsofaffin gwamnonin da karkatar da Naira tiriliyan 2.187 a tsawon shekaru 25.
A cewar rahotan, ana kan binciken tsofaffin gwamnonin, wadanda suka fito daga yankuna shida na kasar, yayin da wasu har an gurfanar da su gaban kuliya.
EFCC ta saki sunayen tsofaffin gwamnoni?
Sai dai a wata sanarwa a ranar Lahadi, kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana wannan rahotan a matsayin 'labarin karya da yaudara'.
Hukumar ta ce ba ta fitar da wannan jerin sunayen ba, kuma ba ta tattauna kan binciken tsofaffin gwamnoni da wata kafar yada labarai, jaridar The Cable ta ruwaito.
Oyewale a cikin sanarwar ya ce:
“Muna yin kira ga jama’a da su yi watsi da wannan rahoton domin karya ne kuma yaudara ce. Wadanda suka wallafa rahoton ne kadai suka san manufar da suke son cimmawa.
"An shawarci kafafen yada labarai da su yi kokarin tabbatar da sahihancin labari kafin bugashi domin kauce wa yaudarar jama'a ta hanyar yada rahotannin karya."
Takaddamar EFCC da wasu tsofaffin gwamnoni
A baya mun ruwaito hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta binciki wasu tsofaffin gwamnoni bisa zargin almundahana da dukiyar jama'a.
Daga cikin su akwai tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ake tuhumarsa da laifuka 19 da suka hada da karkatar da kudade har Naira biliyan 80.2.
Legit Hausa ta tattaro jerin wasu tsofaffin gwamnoni da suka kai ruwa rana da jami'an hukumar EFCC a lokacin da aka yi yunkurin kama su.
Asali: Legit.ng