An Tafka Babban Rashi Bayan Mutuwar Tsohon Minista a Najeriya
- Jihar Delta ta shiga jimami bayan mutuwar tsohon karamin Ministan ilimi, Cif Kenneth Gbagi a jiya Asabar 4 ga watan Mayu
- Marigayin wanda ya tsaya takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar SDP ya kasance babban ɗan kasuwa a fadin jihar
- Tsohon gwamnan jihar Delta, Cif James Ibori ya tabbatar da mutuwar tsohon Ministan inda ya yi masa addu'ar samun rahama
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Delta - An shiga jimami bayan tsohon karamin Ministan ilimi, Cif Kenneth Gbagi ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 62.
Gbagi ya yi takarar gwamnan jihar Delta a zaben da aka gudanar a shekarar 2023 da ta gabata.
Takarar marigayin a zaben gwamnan Delta
Marigayin ya yi takara a jam'iyyar adawa ta SDP a zaben wanda ya kasance daya daga cikin manyan masu neman kujerar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan jihar Delta, Cif James Ibori ya tura sakon jaje ga iyalan marigayin inda ya yi masa addu'ar samun rahama.
Ibori ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a jiya Asabar 4 ga watan Mayu inda ya ce yi addu'ar Ubangiji ya jikansa.
"Olorogun Kenneth Gbagi. Abovwolovwolo. Atighoyowa. Ka tafi kenan, ubangji ya jikanka ya sa ka huta.”
- James Ibori
Sanarwa daga iyalan marigayin
Babban ɗan marigayin, Emuoboh Gbagi ya fitar da sanarwa kan mutuwar mahaifin nasu a madadin iyakansa gaba daya.
Emuoboh ya ce tsohon ministan ya rasu ne a jiya Asabar 4 ga watan Mayu yana da shekaru 62 a duniya.
Marigayin kafin rasuwarsa ya kasance babban ɗan kasuwa wanda ya mallaki otal na Four-Star da kuma manyan kantuna a Warri da kuma karamar hukumar Effurun a jihar.
Zulum ya tafka babban rashi a Borno
A wani labarin, kun ji cewa hadimin Gwamna Babagana Umara Zulum ya riga mu gidan gaskiya a Maiduguri.
Marigayin mai suna Cif Kester Ogualili ya riƙe muƙamin hadimin gwamnan a bangaren harkokin al'umma.
Ogualili ya fito ne daga karamar hukumar Dunukofia a jihar Anambra wanda ya shafe tsawon rayuwarsa a jihar Borno.
Asali: Legit.ng