UTME: Yadda Makarantar Islamiyya Ta Horas da Ɗalibanta Suka Yi Bajinta a Jarrabawa

UTME: Yadda Makarantar Islamiyya Ta Horas da Ɗalibanta Suka Yi Bajinta a Jarrabawa

  • Yayin da ake ci gaba da samun sakamakon jarrabawar UTME, wata makaranta a jihar Bauchi ta samu zakwakuran dalibai da suka yi bajinta
  • Daliban Makarantar Islamic Orientation da ke Azare a jihar Bauchi da dama sun samu maki fiye da 300 yayin da wasu suka samu fiye da 200
  • Legit Hausa ta tattauna da shugaban makarantar, Aminu Bashir inda ya bayyana irin hanyoyin da suke bi wurin samun nasarar jarrabawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Makarantar Islamic Orientation da ke garin Azare a jihar Bauchi ta yi abin a jinjina mata a jarrabawar UTME a bana.

Bayan fitar da jarrabawar UTME, an samu dalibai da dama da suka tashi da maki mai kyau a makarantar bayan jajircewa da malaman su ka yi.

Kara karanta wannan

UTME 2024: Gwamnan Kwara ya mika sako ga daliban da suka ci mai yawa a JAMB

Daliban Makarantar Islamiyya a Bauchi sun yi kaca-kaca da jarrabawar UTME
Makarantar IOSSA a Bauchi ta horas da dalibanta da suka yi bajinta a jarrabawar UTME. Hoto: IOSSA Bauchi, JAMB.
Asali: UGC

IOSSA ta yi kokari a jarrabawar UTME

Shugaban makarantar, Aminu Bashir shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa yayin tattaunawarsu kan sakamakon jarrabawar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin daliban da suka fi cin jarrabawar akwai:

1. Abdullahi Aliyu Garba: 347.

2. Umar Magaji: 330.

3. Abdurrahman Bala Bako: 305.

4. Sadiq Adamu Bakoji: 289.

5. Rabiatu Adamu Galdimari: 282.

6. Aishatu Yusuf Adamu: 277.

7. Abdullahi Abdul kadir Shehu: 277.

8. Ibrahim Muhammad: 276.

9. Suleiman Bala Gagarau: 275.

10. Ahmad Inuwa Indawatu: 252.

11. Musaddaq Sadiqu Isah: 242.

12. Adamu Umar Yusuf: 242

Shugaban makarantar ya ce babban musabbabin samun nasarar su shi ne ba su yarda da ba dalibai amsa a jarrabawa ba ta kowace hanya.

Sannan ya ce suna ba dalibai horaswa na musamman saboda tunkarar jarrabawa na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Ganduje: Yadda dakatarwa a mazaba ta kori shugabanni 3 a APC da PDP ana ji ana gani

Aminu ya fadi sirrin cin jarrabawar UTME

"Na farko babban sirrin da muka yi imani da shi a jarrabawa shi ne bamu yarda da ba dalibai amsa ba ko kuma kowane irin taimako sai dai su shiga dakin jarrabawa mu barsu da halinsu."
"Sannan mu na ba su horaswa na musamman a makaranta wurin ba su tambayoyin da suka wuce suna amsa su."
"Muna amfani da dakunan kwamfuta domin basu damar amsa tambayoyin da suka gabata, dalibi zai amsa su ya sami amsa nan take idan kuma bai ci zai sake bita domin sake gwadawa har ya yi nasara."

- Aminu Bashir

Har ila yau, ya ce tsofaffin daliban makarantar da suke karatu a jami'o'i da ke tsangayar likitance suna matukar taimakawa dalibai idan sun sami hutu.

Ya bayyana yadda ɗaliban makarantar suka samu guraben karatu a Jami'o'i daban-daban wanda ya ce da yawansu sun ba da gudunmawa sosai a makarantar.

Kara karanta wannan

"Buhari ya daura shugaban APC duk da zargin cin N15bn", Tsohon Minista ya tona asiri

Fatima Alkali ta yi bajinta a UTME

Kun ji cewa wata matashiyar ɗaliba daga jihar Yobe ta burge 'yan Najeriya bayan fitar da sakamakon jarrabawar UTME.

Dalibar ta samu maki 336 a jarrabawar wanda ta kasance sahun gaba-gaba cikin dalibai a Arewacin Najeriya baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.