An Rasa Rayuka Bayan Bam Ya Tashi da 'Yan Kai Amarya a Borno
- An yi rashin rayukan mutane 11 bayan bam da ƴan ta'adda suka dasa ya tashi da motocinsu a jihar Borno
- Daga cikin waɗanda suka ransu akwai mutum 9 waɗanda jami'an CJTF ne waɗanda suka rasu a ƙaramar hukumar Gamboru-Ngala
- A ƙaramar hukumar Dikwa wani ƴan bam ya tashi da motar ƴan kai amarya inda mutum.biyu suka rasa rayukansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Aƙalla mutane 11 ne suka mutu yayin da biyar suka jikkata bayan wasu motoci biyu sun taka bam da aka binne a ƙananan hukumomin Gamboru-Ngala da Dikwa na jihar Borno cikin makon da ya gabata.
Waɗanda suka mutu sun haɗa da jami’an CJTF guda tara, waɗanda suka rasa ransu a ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu a ƙaramar hukumar Gamboru-Ngala, cewar rahoton jaridar Leadership.
Sauran kuma su ne wasu fararen hula biyu, waɗanda suka mutu a ranar Asabar, 4 ga watan Mayu a ƙaramar hukumar Dikwa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An hallaka jami'an CJTF
Kakakin CJTF na jihar Borno, Bashir Abbas, ya bayyana cewa:
"Jami’an mu sun fito ne daga Ngala da yammacin makon jiya Asabar, kuma a wajen garin ne motarsu ta bi ta kan wani bam da ake kyautata zaton ƴan ta’adda ne suka binne shi."
"Mutum tara daga cikinsu sun mutu nan take, biyu kuma sun samu munanan raunuka kuma an garzaya da su asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri."
Bam ya tashi da ƴan kai Amarya
Wani majiya daga rundunar ƴan sandan jihar Borno ya bayyana cewa wata mota ta taka bam a ƙaramar hukumar Dikwa ta jihar a ranar Asabar, 4 ga watan Mayun 2024.
A kalamansa:
"Da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Asabar, 4 ga watan Mayu, wata mota ƙirar Honda SUV ta taka wani bam tsakanin Dikwa da Damno a ƙaramar hukumar Dikwa, mutum biyu sun mutu tare da raunata wasu uku, dukkansu fararen hula."
Sai dai, wani shaidar gani da ido, Rawa Fannami, wanda mazaunin Dikwa ne ya ce mutum biyar ne suka mutu.
Rawa Fannami ya yi bayanin cewa motar na cikin ayarin ƴan ɗaukar amarya ne daga Damno zuwa Dikwa, amma ba ita ba ce ta ɗauko amaryar.
Ya bayyana cewa waɗanda suka rasa ransu sai dai aka tattara abin da ya yi saura a jikinsu a cikin buhuna domin binne su.
Bam ya hallaka mutane a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa ana fargabar aƙalla mutane 10 sun mutu sakamakon tashin wani bam da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka dasa a titin Baga-Kukawa a jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a lokacin da wata motar bas ta haya ta taka Bam ɗin kuma ya tashi, bayan mutanen da suka mutu, wasu kusan 20 sun ji raunuka daban-daban.
Asali: Legit.ng