Jerin Jihohin Najeriya da Arzikin da Kowace Ta Mallaka Ta Fuskar Alkaluman GDP
Abuja - A wata mazhabar, masana ilmin tsimi su kan auna karfin tattalin arziki da ma’aunin GDP wanda shi ne jimillar arziki.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Alkaluman da aka samu daga shekarar 2022 sun nuna arzikin da kowace jihar kasar nan ta mallaka, inda aka ga Legas ce a gaba.
Karfin tattalin arzikin jihohin Najeriya
Bayanan da aka samu daga The Cable a dandalin X sun nuna cewa jihohin da suka fi arziki sun yi tarayya a wajen mallakar mai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karfin tattalin arzikin Legas kadai ya zarce Naira tiriliyan 40 tun a shekarar 2022. Jihar ce kan gaba wajen samun kudin shiga a yau.
Jihohin da ke yankin Neja-Delta; Ribas, Akwa Ibom, Delta da Bayelsa suna sahun gaba.
Legit ta yi nazarin alkaluman, ta lura cewa Ekiti, Ebonyi a Enugu su ne jihohin kudancin kasar nan mafi karancin karfin tattali.
Tattalin arziki: Matsayin jihohin yankin Arewa
A yankin Arewacin Najeriya, jihar Neja ce ake lissafin ta fi kowace karfin arziki, daga nan kuma sai Kaduna da ke makwabtaka da ita.
Benuwai mai arzikin noma ta sha gaban Kano da akalla Naira biliyan 700. Kogi, Katsina da Sokoto ne suka rufe jihohi 20 na farko.
Borno, Nasarawa, Kebbi, Zamfara, Kwara da Yobe sune jihohin da ke karshe idan ana zancen karfin tattalin arziki ta GDP a Najeriya.
Jihohin da suka fi karfin tattalin arziki
1. Lagos: N41.17trn
2. Rivers: N7.96trn
3. Akwa Ibom: N7.77trn
4. Imo: N7.68trn
5. Delta: N6.19trn
6. Anambra: N5.14trn
7. Ondo: N5.10trn
8. Ogun: N5.03trn
9. Bayelsa: N4.63trn
10. Niger: N4.58trn
11. Kaduna: N4.31trn
12. Benue: N4.27trn
13. Kano: N4.20trn
14. Cross River: N4.07trn
15. Edo: N3.99trn
16. Kogi: N3.69trn
17. Oyo: N3.65trn
18. Abia: N3.53trn
19. Katsina: N3.32trn
20. Sokoto: N2.85trn
21. Adamawa: N2.66trn
22. Bauchi: N2.63trn
23. Ekiti: N2.35trn
24. Osun: N2.30trn
25. Ebonyi: N2.24trn
26. Jigawa: N2.16trn
27. Gombe: N2.10trn
28. Taraba: N2.04trn
29. Borno: N1.96trn
30. Nasarawa: N1.86trn
31. Kebbi: N1.80trn
32. Zamfara: N1.73trn
33. Plateau: N1.50trn
34. Enugu: N1.45trn
35. Kwara: N1.38trn
36. Yobe: N1.09trn
<BudgIT 2022>
Tsohon Mataimakin gwamna ya dauke motoci
Rahoto ya zo cewa tsohon mataimakin gwamnan Edo ya tubure, ya ki dawo da motoci bayan 'yan majalisa sun tsige shi a mulki.
‘Dan siyasar ya ce mota guda kurum ya samu a tsawon shekaru kusan takwas mataimakin gwamna a karkashin Godwin Obaseki.
Asali: Legit.ng