Yadda aka samo sunayen jihohi 36 na Najeriya
Akwai tsohon tarihi a kan sunan kowacce jiha a kasar Najeriya. Daga sunayen rafuka zuwa na sadaukai, ga yadda sunayen dukkan jihohin kasar nan suka samo asali.
1. Abia
An samo sunan jihar nan ne daga hada kalmar farko ta kabilu hudu na jihar a shekarar 1991. Aba, Bende, Isuikwuato da Afikpo.
2. Adamawa
Jihar Adamawa ta samo sunanta ne daga sadauki, Modibbo Adama Bin Ardo Hassan, wanda ya ci garin da yaki a farkon karni na 19.
3. Akwa-Ibom
An samao sunan jihar ne daga kogin Qua Iboe ko kuma Kwa Iboe.
4. Anambra
Jihar Anambra ta samo sunanta ne bayan sauya sunan wani kogi fitacce a yankin da aka yi. Sunan kogin Oma Mbala ko Anyim Oma Mbala.
5. Bauchi
Kalmar Bauchi, kalmar Hausa ce mai nufin gefen tsaunika na kudanci. Kabilun da ke rayuwa a yankin kudanci na kasar Hausa ana kiransu da 'kasashen Bauchi'. Daga bisani aka fara kiran yankin da Bauchi.
A daya bangaren kuwa, za a iya cewa an samo sunan ne daga Baushe, fitaccen mafarauci wanda ya zauna a yankin a karni na 19.
6. Bayelsa
Bayelsa an samo sunanta ne bayan hada sunayen kananan hukumomi uku na tsohuwar jihar Ribas. Su ne karamar hukumar Balga, Yenegoa da Salga. Hakan ne ya tashi ya bada Bayelsa.
7. Benue
An samo suna jihar Benue ne bayan da aka mayar da kalmar Binuwe ta turanci. Ma'anarta kuwa shine 'tushen ruwa'.
8. Borno
Borno wani suna ne na jama'ar kabilar Kanuri, wadanda sune suka mamaye jihar Borno. Hakan yasa aka saka wa jihar sunan kabilarsu.
9. Cross River
Jihar ta samo sunanta ne daga wani kogi mai suna Oyono ko Cross River.
10. Delta
A wannan jihar ne kogin Neja ya hadu da tekun Atlanta, wannan ne yasa ake kiranta da Delta.
11. Ebonyi
An samo sunan ne daga kalmar Aboine, sunan wani rafi ne da ya ratsa Abakaliki, babban birnin jihar.
12. Edo
Jama'ar kabilar Bini da ke rayuwa a yankin, ana kiransu da Edo ko Iduu. Wannan ne yasa aka sanya wa jihar suna Edo.
13. Ekiti
Okiti kalma ce da ke da ma'anar wurin da ke zagaye da tsaunika. Hakan ne yasa daga baya ake kiran jihar da Ekiti.
14. Enugu
Saboda tsaunikan da ke yankin, jama'a kabilar Ibo na kiran wurin da "Enu Ugwu", ma'anarsa kuwa "Saman tsaunika".
15. Gombe
Gombe kalma ce daga kabilar Fulfulde, wanda shine yaren da mafi yawan mazauna jihar ke yi.
16. Imo
Kamar dai sauran fitattun jihohi a Najeriya, Imo ta samo sunanta ne daga kogin Imo Mmiri.
17. Jigawa
Jihar Jigawa ta samo sunanta ne daga yanayin kasar wurin.
18. Kaduna
Kaduna kalma ce mai nufin Kada amma a jam'i. Jihar ta samo sunanta ne daga kogin Kaduna wanda ke kunshe da Kaduna.
19. Kano
Kano ta samo sunanta ne daga wani makeri dan kabilar Gaya wanda ya fara zama a yankin a yayin da yake neman karfe. An saka wa jihar sunansa kacokan.
20. Katsina
An saka wa jihar sunanta ne saboda matar wani fitaccen basarake mai suna Janzama. Sunan matarsa Katsina.
21. Kebbi
Kebbi ta samo sunanta ne daga dakin Allah na Ka'abba da ke garin Makka a kasar Saudi Arabia.
KU KARANTA: Turmi da tabarya na kama shi da diyarsa, shiyasa na rabu da shi - Matar basarake
22. Kogi
Tun bayan da aka samu haduwar rafuka biyu a jihar, rafin Neja da Binuwai, Hausawa ke kiran yankin da Kogi.
23. Kwara
A lokaci mai tsawo da ya shude, ana kiran kogin Neja ne da kogin Kwara wanda kuwa nupawa ne da ke iyakar jihar ke kiransa da hakan.
24. Lagos
A shekarar 1472, turawan farko da suka saka kafafunsu a jihar Legas, 'yan asalin kasar Fotugal ne. Saboda yawan rafukan da ke garin, sun kira shi da Legas wanda suka samo daga 'Lake', ma'anar tafki.
25. Nasarawa
Nasarawa a hausance yana nufin nasara. An samo sunan jihar ne daga masarautar Nasarawa wacce Makama Dogo ke shugabanta.
26. Niger
Neja ta samo sunanta ne daga kogin Neja.
27. Ogun
Ogun ta samo sunanta ne daga kogin Ogun.
28. Ondo
Ondo kalma ce mai nufin baki, an saka mata sunan ne sakamakon bakin jama'ar masarautar Ondo da suka zauna a yankin
29. Osun
Wannan jihar ta samo sunanta ne daga kogin Osun.
30. Oyo
An samo sunan jihar ne daga tsohuwa masarautar Oyo.
31. Plateau
An samo sunan jihar Filato ne daga Jos Plateau.
32. Rivers
Wannan jihar ta samo sunanta ne sakamakon yawan tafkuna, kogi da rafukan da ke yankin.
33. Sokoto
Jihar Sokoto ta samo sunanta ne daga kalmar kasuwa ta larabci, wato 'Suk'. An saka wa jihar sunan ne tun bayan kafuwar daular Musulunci.
34. Taraba
Jihar Taraba ta samo sunanta ne daga kogin Taraba.
35. Yobe
An samo sunan jihar Yobe ne daga wani kogi mai suna Waube ko Ouobe. Daga nan ne aka samo sunan Yobe.
36. Zamfara
An samo sunan jihar ne daga harshen mazauna yankin na Zamfarawa, daya daga cikin mazauna yankin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng