Karshen 'Yan Bindiga Ya Zo, Gwamna Ya Shirya Sanya Hannu a Wata Doka, Ya Yi Gargadi

Karshen 'Yan Bindiga Ya Zo, Gwamna Ya Shirya Sanya Hannu a Wata Doka, Ya Yi Gargadi

  • Yayin da 'yan bindiga suka kai mummunan hari a jihar Kebbi, Gwamna Nasir Idris ya shirya kawo karshensu gaba daya
  • Gwamnan ya ce zai sanya hannu a dokar kisan kan duk wadanda aka kama da ba mahara bayanai domin cutar da al'umma
  • Gwamnan ya bayyana haka yayin jaje a kauyen Tudun Bichi a karamar hukumar Danko-Wasagu bayan harin 'yan bindiga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya ce ba zai yi wata-wata ba domin kawo karshen 'yan yadda a jijar.

Kwamred Nasir ya ce zai tabbatar da dokar da za ta ayyana kisa kan duk masu ba 'yan bindiga bayanai a jihar.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba bayan 'yan bindiga sun shiga garuruwan Katsina, an hallaka mutane 24

Gwamna ya sha alwashin kawo karshen 'yan bindiga a jiharsa
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi zai sanya hannu a wata doka game da 'yan bindiga. Hoto: Nasir Idris.
Asali: Facebook

Gwamna ya sha alwashi kan 'yan bindiga

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin jaje a kauyen Tudun Bichi a karamar hukumar Danko-Wasagu kan hare-haren 'yan bindiga, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi alkawarin ba jami'an tsaro dukkan goyon baya domin tabbatar da samun nasara a dakile 'yan ta'addan, cewar Daily Post.

"Ayyukan masu ba 'yan bindiga bayanan sirri ya saba tsarin al'adu har ma da addini."
"Wasu marasa tausayi kawai za su dauki bayanai masu muhimmanci su ba 'yan bindiga domin kai hare-hare ga bayin Allah."
"Ba zan taba barin haka ya ci gaba da faruwa ba, masu irin wanna hali su sani idan aka kama su, zan dabbaka dokar hukuncin kisa kansu nan take."

- Nasir Idris

Martanin Dagacin gari kan harin 'yan bindiga

Dagacin kauyen Tudun Bichi, Muhammad Mika'ilu ya godewa gwamnan kan wannan ziyara da ya kawo musu.

Kara karanta wannan

"Ya kware a cin amana": APC ta ja kunnen Tinubu kan sake jiki da gwamnan PDP

Mikailu ya ce hare-haren da bindiga ya hana su yin noma kusan shekaru biyu kenan a ƙauyen.

Ya bukaci Gwamna da ya taimaka a karo musu jami'an tsaro a yankin domin samar da tsaro mai inganci.

'Yan bindiga sun hallaka mutane 24

Kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun sake kai mummunan hari jihar Katsina inda suka hallaka mutane 24 yayin farmakin.

Maharan sun kai harin ne a unguwar Sarkin Noma da ke karamar hukumar Sabuwa a jihar a daren ranar Alhamis 2 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.