'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an Tsaro a Wani Kwanton Bauna a Jihar Zamfara
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi wa jami'an tsaron jihar Zamfara waɗanda aka fi sani da Askarawan Zamfara kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Maradun
- Miyagun ƴan bindigan sun hallaka jami'ai uku a farmakin da suka kai musu a unguwar Jambako lokacin da suke kan hanyar zuwa wani gari
- Wani majiya ya bayyana cewa tsagerun sun yi awon gaba da makamai tare da baburan jami'an tsaron bayan kai musu harin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun yi wa jami’an rundunar tsaron jihar Zamfara (CPG) waɗanda aka fi sani da Askarawan Zamfara kwanton ɓauna.
Ƴan bindigan sun hallaka jami'an rundunar mutum uku bayan sun yi musu kwanton ɓauna a unguwar Jambako da ke ƙaramar hukumar Maradun a jihar.
Wani majiya mai suna Sanusi Muhammad ya shaida wa wakilin jaridar Leadership cewa ƴan bindigan sun yi wa jami’an na CPG kwanton ɓauna a Tungar Nayarciga kan hanyarsu ta zuwa garin Faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, ƴan bindigan sun kuma kwashe makamansu da baburansu.
Harin ya haifar da tashin hankali da fargaba a tsakanin mazauna yankin.
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, kan sabon harin da ƴan bindigan suka kai kan jami'an tsaron.
Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa bai samu rahoto kan aukuwar lamarin ba amma zai bincika ya gani.
A kalamansa:
"Eh gaskiya ban samu rahoto kan hakan ba amma zan bincika lamarin na gani."
Sai dai, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba a sake jin komai daga gare shi ba.
Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Dauran da garin Zurmi, hedkwatar ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Ƴan bindigan a yayin harin sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba.
Tsagerun ƴan bindigan sun kuma ƙona ƙarfen samar da sabis na MTN a garin, wanda hakan ya haifar da yankewar kafar sadarwa.
Asali: Legit.ng