Digiri Dan Kwatano: Gwamnatin Tarayya Ta Juyo Kan Masu Takardun Bogi a Najeriya
- Ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman, ya ce gwamnatin tarayya za ta bankaɗo mutanen da ke da takardun bogi a Najeriya, bayan kammala bincike da aka yi a digirin bogi
- Tahir Mamman ya jaddada buƙatar kiyaye mutuncin ilimi tare da yin alƙwarin haɗa gwiwa da hukumomin da abin ya shafa domin dawo da martabar tsarin
- Ministan dai ya bayyana hakan ne lokacin da ya ƙarbi rahoton binciken kwamitin da aka kafa domin bin diddigin masu digirin bogi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ma’aikatar ilimi ta sha alwashin gano mutanen da ke amfani da takardun shaidar karatu na bogi a Najeriya.
Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a lokacin da yake karɓar sakamakon kwamitin bincike kan digirin bogi a ofishinsa da ke Abuja a ranar Juma’a 3 ga watan Mayu.
A kwanakin baya ne dai gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai binciki ayyukan jami'o'i masu zaman kansu sama da 100 da wasu jami'o'in ƙasashen waje a Jamhuriyar Benin,Togo, da sauran ƙasashe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ci gaban ya biyo bayan wata fallasa kan yadda ake samun digirin bogi da wani ɗan jaridar Daily Nigerian ya yi.
Tahir Mamman ya sha alwashin tsaftace fannin ilimi a Najeriya yana mai nuna rashin jin daɗinsa da irin abubuwan da aka bankaɗo a lokacin binciken.
Wane mataki za a ɗauka?
Ministan ya ce ma'aikatar ilimi za ta haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa domin tsarkake harkar ilimi daga duk wani abu na yaudara.
Ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da ingancin ilimi, inda ya ce akwai yiwuwar daidaikun mutane da ke riƙe da takardun bogi na yin a cikin sassan gwamnati da masu zaman kansu.
Ministan ya tabbatar da ƙudirin ma'aikatar na aiwatar da matakan dawo da martabar tsarin ilmi a ƙasar nan.
Jaridar The Punch ta ambato ministan na cewa:
"Ta yiwu akwai masu amfani da takardun bogi a a cikin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu waɗanda ya kamata a kore su. Wannan rahoton sakamako ne na cikakken bincike."
Dakatar da digirin wasu ƙasashe
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta dakatar da tantancewa da amfani da takardun shaidar digiri daga jamhuriyar Benin da Togo.
Wannan matakin ya biyo bayan wani rahoto da ya yi bayani dalla-dalla yadda ake samu digiri a wata jami’a a Jamhuriyar Benin cikin kasa da watanni biyu.
Asali: Legit.ng