'Yan Bindiga Sun Hallaka Dagaci a Wani Yanayi Mara Dadi a Kaduna
- Ƴan bindiga waɗanda ake zargin hayarsu aka ɗauko sun tafka ta'asa a wani ƙauye na ƙaramar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna
- Miyagun ƴan bindigan sun hallaka Dagacin ƙauyen Marke da ke gundumar Dandamisa bayan sun shiga har cikin gidansa
- Bayan hallaka Dagacin ƴan bindigan sun kuma bankawa gidansa wuta wanda ya sanya ko gawarsa ba a samu ganowa ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun kashe Malam Kabiru Mohammed, Dagacin ƙauyen Marke da ke gundumar Dandamisa a ƙaramar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna.
Ƴan bindigan waɗanda ake zargin hayarsu aka ɗauko, sun shiga gidan mamacin ne da misalin ƙarfe 12:30 na daren ranar Alhamis sannan suka kori kowa daga harabar gidan.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan sun fara neman Malam Kabiru wanda ke ɓoye a cikin silin tare da ƙaninsa Tukur Mohammed.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa, daga bisani ƴan bindigan sun gano shi sannan suka yi masa yankan rago tare da bankawa gidan wuta.
Marigayi Kabiru Muhammad, mai shekara 30 a duniya, an naɗa shi a matsayin Dagacin garin Marke ne a shekarar 2018.
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Da yake mayar da martani kan lamarin, kansilan gundumar Dandamisa, Alhaji Aminu Sani Marke ya ce ba a iya gano gawar marigayin ba saboda ƙonewar da gidan ya yi.
"Ƴan bindigan sun shafe kusan sa'a ɗaya suna cin karensu babu babbaka a ƙauyen kuma sun tafi da wasu kayayyaki masu daraja na miliyoyin Naira."
- Alhaji Aminu Sani Marke
Ko da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Kakakin ya bayyana cewa rundunar na ci gaba da gudanar da bincike domin zaƙulo masu hannu a lamarin.
Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa Yan bindiga sun sake kai mummunan hari a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Maharan nan sun hallaka mutane da dama a Kakangi da Unguwar Matinja sannan suka yi awon gaba da wasu mutum masu sarautar gargajiya.
Asali: Legit.ng