An Ba da Labarin Boyayyen Kirki da Son Musuluncin Tsohuwar Ministar Buhari

An Ba da Labarin Boyayyen Kirki da Son Musuluncin Tsohuwar Ministar Buhari

  • Gbemisola Ruqayyat Saraki ta cika shekara 59 a duniya, wannan lamari ya jawo aka tona ayyukan alherin da ta ke yi
  • A ranar da ake murnar zagayowar lokacin haihuwar ta ne aka gane yadda ‘yar siyasar ta taimakawa makwabtanta
  • Wani mazaunin unguwar Maitaima ya shaidawa Legit yadda Gbemisola Saraki ta rika tura mutane zuwa aikin hajji

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A ranar 5 ga watan Mayun 2024, tsohuwar Minista, Gbemisola Ruqayyat Saraki ta cika shekara 59 da haihuwa a duniya.

‘Danuwanta watau Dr. Abubakar Bukola Saraki ya yi amfani da shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter, ya taya ta murna a jiya.

Gbemisola Ruqayyat Saraki
Tsohuwar Ministar sufuri,Gbemisola Ruqayyat Saraki ta na taimakon musulmai a Abuja Hoto: @BukolaSaraki/Getty Images
Asali: UGC

Bukola Saraki da Gbemisola Saraki

Kara karanta wannan

Gwamna ya naɗa tsohon shugaban sojojin Najeriya a shirgegen mukami a jiharsa

Tsohon shugaban majalisar dattawan wanda ya yi gwamnan Kwara ya taya Gbemisola Ruqayyat Saraki murnar zagayowar ranar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da Bukola Saraki yake cikin jiga-jigai a APC, kanwar tasa wanda ta rike karamar ministar sufuri tana cikin manya a APC.

Gbemi Saraki: An yaba alheran tsohuwar minista

Maganar da tsohon gwamnan ya yi ne ya jawo wani bawan Allah ya rika yabon wannan mata, yana jero wasu ayyukan alheranta.

Baba Bala Katsina wanda ma’abocin shafin X ne, ya ce Gbemisola Ruqayyat Saraki ta biyawa mutane da-dama kujerun aikin hajji.

Da mu ka nemi jin ta bakin wannan mutumi, ya shaida mana cewa sun zauna wuri daya da tsohuwar Ministar a Maitaima a Abuja.

Malam Baba Bala Katsina ya ce da farko babu masallaci a layin Panama a unguwar Maitama, sai daga baya ne wani ya gina masu.

Kara karanta wannan

Badakalar N80bn: Abin da wasu tsofaffin gwamnoni ke cewa game da Yahaya Bello

A dalilin masallacin musulmai suka rika samun damar taruwa suyi salloli da sauran ibada.

Wanda ya gina masallacin makwabcin Sanata Gbemisola Saraki ne kuma ya rasu a yanzu kamar yadda bayanai suka zo ga Legit.

Gbemisola Saraki ta biyawa mutane kujerar hajji

Kamar yadda ya shaida mana, Gbemisola Saraki ta biyawa limamin wannan masallaci kujerar aikin hajji zuwa kasa mai tsarki.

A sanadiyyar ‘yar siyasar, wannan limami wanda mutumin yankin Arewa maso gabas ne, ya samu damar sauke faralin musulunci.

Akwai wasu bayin Allah biyu daga gida guda wanda tsohuwar Ministar ta biya masu hajji.

Sauran ayyukan neman ladan Gbemisola Saraki

Abin alherin na ta bai tsaya a nan ba, wannan mutumi wanda masanin tarihi ne ya shaidawa Legit ta kai wani direba Saudi Arabiya.

Bayan kujerun hajji, Sanata Saraki ta kan kashe dukiya wajen rabon raguna a lokacin da ake shirin babban sallah domin a yi yin layya.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya 'fallasa' babban dalilin rikicin Nyesom Wike da sabon Gwamnan Ribas

Albarkar zuri'ar Malam Musa Yar’adua

Malam Musa Yar’adua shi ne Matawallen Katsina, a gidansa aka samu Shehu Yar’adua, Ummaru Yar’adua da Abdulaziz Yar’adua.

Ana da labarin yadda Murtala Shehu Musa Yar’adua ya rike karamin ministan tsaro a 2010 zuwa lokacin da aka canza ministoci a 2011.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng