Badakalar N2.1trn: Jerin Tsofaffin Gwamnoni 54 da EFCC Ke Tuhuma Kan Zargin Almundahana
FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa ta na binciken zargin badakala da tsofaffin gwamnoni 54 suka yi a Najeriya.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Ana zargin tsofaffin gwamnonin sun karkatar da N2.187trn a cikin shekaru 25 da aka yi tun bayan dawowa dimukradiyya.
EFCC na zargin tsoffin gwamnoni 54
Kamar yadda Vanguard ta tattaro, ba a hada da sauran kadarori da aka kwato ba wanda yawan kuɗin ya kai biliyoyin Naira.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yawan kudi da ake zargin an sace ya kai kasafin kudin jihar Legas na shekarar 2024 (N2.25trn) sannan ya kai kasafin kudin dukkan jihohin Kudu maso Gabas guda biyar (N2.29trn).
Har ila yau, kudin ya fi kasafin kudin jihohin Arewa maso Gabas da kuma Arewa ta Tsakiya, cewar Journalist101.
Daga cikin tsoffin gwamnoni 58 wasu ana kan bincike yayin da wasu kuma aka kammala bincike da kuma hukunta su.
Tsoffin gwamnonin da EFCC ke zargi sun fito daga yankuna shida da muke da su a ƙasar daga Kudu har Arewa wanda suka haɗa da:
Tsoffin gwamnonin da EFCC ke zargi
1. Marigayi Abubakar Audu (N10.966 bn) - Kogi
2. TA Orji and 'ya'yansa (N551 bn) - Abia
3. Yahaya Bello (N80.2 bn) - Kogi
4. Chimaroke Nnamani (N5. 3 bn) - Enugu
5. Sullivan Chime (N450 million) - Enugu
6. Kayode Fayemi (N4bn) - Ekiti
7. Ayo Fayose (N6.9 bn) - Ekiti
8. Abdullahi Adamu (N15bn) - Nasarawa
9. Danjuma Goje (N5bn) - Gombe
10. Aliyu Wamakko (N15 bn) - Sokoto
11. Sule Lamido (N1.35 bn) - Jigawa
12. Joshua Dariye (N1. 16 bn) - Plateau
13. Timipre Sylva (N19.2 bn). - Bayelsa
14. Saminu Turaki (N36bn) - Jigawa
15. Orji Uzor Kalu (N7. 6bn) - Abia
Sauran sun hada da:
16. Bello Matawalle (N70 bn) - Zamfara
17. Lucky Igbinedion (N4. 5 bn) - Edo
18. Rabi'u Kwakwanso (N10bn) - Kano
19. Peter Odili (N1000 bn) - Rivers
20. Jolly Nyame (N1.64 bn) - Taraba
21. James Ngilari (N167m) - Adamawa
22. Abdulaziz Yari (N84 bn) - Zamfara
23. Godswill Akpabio (N100bn) - Akwa Ibom
24. Abdul fatah Ahmed (N9 bn) - Kwara
25. Ali Mode-Sheriff (N300bn) - Borno
26. Willie Obiano (N43 bn) - Anambra
27. Ibrahim Dankwambo (N1. 3bn) - Gombe
28. Darius Ishaku (N39bn) - Taraba
29. Ramalan Yero (N700m) - Kaduna
30. Achike Udenwa (N350m) - Imo
Sai kuma:
31. Rochas Okorocha (N10. 8bn) - Imo
32. James Ibori (N40 bn) - Delta
33. DSP Alamieyeseigha ((N2.655bn) - Bayelsa
34. Gabriel Suswam (N3. 111bn) - Benue
35. Samuel Orton (N107bn) - Benue
36. Murtala Nyako (N29bn) - Adamawa
37. Rashid Ladoja (4.7bn) - Oyo
38. Christopher Alao-Akala (N11. 5 bn) - Oyo
39. Marigayi Abdulkadir Kure (N600m) - Niger
40. Babangida Aliyu (N4bn) - Niger
Sannan akwai:
41. Abubakar Audu (N10bn) -. Kogi
42. Idris Wada (N500m) - Kogi
43. Ibrahim Shekarau (N950m) - Kano
44. Adamu Aliero (N10bn) - Kebbi
45. Usman Dakingari da matarsa (N5. 8bn) - Kebbi
46. Attahiru Bafarawa (N19. 6bn) - Sokoto
47. Jonah Jang (N6. 3bn) - Plateau
48. Aliyu Doma (N8bn) - Nasarawa
49. Tanko Al’Makura (N4bn) - Nasarawa
50. Boni Haruna (N93bn) - Adamawa
51. Bindow Jibrila (N62bn) - Adamawa
52. Adamu Muazu (13bn) - Bauchi
53. Isa Yuguda N212bn) - Bauchi
54. Mohammed Abubakar (N8. 5bn) - Bauchi.
EFCC ta yi garambawul a mukamai
Kun ji cewa Hukumar EFCC ta yi garambawul a muƙamai a kokarin kawo sauyi domin ci gaba da yaki da cin hanci a Najeriya.
Wannan nadin mukamai da sauye-sauye na zuwa ne yayin da hukumar ke tuhumar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello kan badakalar N84bn.
Asali: Legit.ng