An Samu Barkewar Wata Cuta a Adamawa, Mutum 42 Sun Rasa Ransu
- An samu ɓullar cutar Kyanda a wasu ƙananan hukumomi biyu na jihar Adamawa wacce ta yi sanadiyyr rasuwar mutum 42
- Kwamishinan lafiya na jihar wanda ya tabbatar da hakan ya ce cutar ta ɓarke ne a gundumomi 15 na ƙananan hukumomin Mubi da Gombi na jihar
- Kwamishinan ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihsr ta ɗauki matakan kariya a sauran ƙananan hukumomin jihar domin daƙile yaɗuwar cutar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - Gwamnatin jihar Adamawa a yammacin ranar Juma’a ta tabbatar da cewa mutum 42 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar kyanda.
Kwamishinan lafiya na jihar Felix Tangwame, wanda ya bayar da ƙarin bayani kan ɓullar cutar, ya ce an samu asarar rayuka a ƙananan hukumomin Mubi da Gombi.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Yola, babban birnin jihar, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ya bayyana cewa cutar kyanda ta ɓarke a gundumomi takwas a ƙaramar hukumar Mubi da gundumomi bakwai a ƙaramar hukumar Gombi.
Ya kuma bayyana cewa mutum 42 daga cikin 131 da suka kamu da ita a Mubi da mutum 177 da suka kamu da ita a Gombi ne suka rasu, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Wane ƙoƙari gwamnati ke yi?
A wani mataki na kaucewa yaɗuwar cutar, kwamishinan ya ce an ɗauki matakan kariya a dukkanin ƙananan hukumomin jihar.
Felix Tangwame ya ce ma’aikatarsa bayan samun rahoton ɓullar cutar, ta mayar da martani cikin gaggawa, lamarin da ya sa ta samu nasarar shawo kan lamarin.
Ya ƙara da cewa gwamnati da takwarorinta na ci gaba ƙoƙari domin shawo kan lamarin.
Bakuwar cuta ta ɓulla a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta NCDC ta tabbatar da ɓullar wata baƙuwar cuta a jihar Sokoto.
Hukumar ta ce mutu huɗu sun rasu sakamakon ɓullar cutar wacce ba a san asalinta ba yayin da ake zargin kusan mutum 164 ne suka kamu da ita.
Asali: Legit.ng