Gwamanti Na Shirin Kawo Hanyar da Za Jawo Ayi Sallama da Matsalar Lantarki
- Shugaban cibiyar kula da makamashin nukiliya ta Najeriya, Farfesa Yusuf Aminu Ahmed ya ce sun kusa fara samar da lantarki ta hanyar nukiliya
- Yusuf Aminu Ahmed ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu a yayin wani taron makamashi a jihar Kaduna
- Farfesan ya kara da cewa shirye-shirye sun yi nisa sosai kuma a halin yanzu ana jiran sanarwa ne daga shugaban kasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Cibiyar kula da makamashin nukiliya ta kasa (NAEC) ta sanar da cewa an kusa kammala fara samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da nukiliya.
Rahotanni sun sun nuna cewa hukumar za ta yi haɗaka ne da hukumar nazari da samar da makamashi (CERT) da ke jami'ar Ahmadu Bello.
Rahoton jaridar Tribune Online ya nuna cewa hukumomin guda biyu sun shirya tsaf domin karfafa harkar wutar lantarki a fadin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai kwararrun da za su yi aikin?
Shugaban cibiyar NAEC, Farfesa Yusuf Aminu Ahmed ya tabbatar da shirin na su ne yayin bikin cikar shekara 20 da kafa cibiyar binciken makamashin nukilya a Zariya.
Shugaban ya ce cikin shekaru da dama ma'aikatan hukumar sun samu gogewa da za ta basu damar samar da lantarki ta hanyar amfani da nukiliya.
Ya kuma bayyana cewa kudirin tuni ya samu goyon bayan shugaba Bola Tinubu kuma za su yi tarayya da sauran masana nukiliya domin kaiwa ga nasara.
Yaushe za a fara amfani da nukiliya?
Sai dai duk da bai bayyana hakikanin lokacin da za su fara aikin samar da wutar ba, ya ce nan da lokaci komai zai kammala.
Ya kuma ce akwai masana da masu zuba jari daga ƙasashen ketare da suke aiki tare wurin ganin kaiwa ga nasara, cewar Peoples Gazette
A cewar rahoton, a halin yanzu an saka hannu a yarjejeniya tsakanin gwamnatoci, kuma nan gaba kadan shugaba Bola Tinubu zai bada sanarwa da kansa.
Gwamnati za ta cire tallafin lantarki
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da 'yan Najeriya ke kokawa kan cire tallafin man fetur, gwamnatin Bola Tinubu tana shirin daukar sabon mataki a bangaren wutar lantarki.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin wutar lantarki ba sakamakon basussukan da kamfanonin samar da wutar lantarki ke bin kasar.
Asali: Legit.ng