Kurunkus: NSCDC ta yi Ram da Mota Dauke da Lita 20, 000 na Fetur a Kano

Kurunkus: NSCDC ta yi Ram da Mota Dauke da Lita 20, 000 na Fetur a Kano

  • Hukumar tsaron farar hula, NSCDC a Kano ta bayyana dakume wasu da ke kokarin safarar tankar mai zuwa jihar Katsina yayin da ake tsaka da wahalar mai
  • NSCDC ta kama tankar man ne a titin Ibrahim Taiwo an makare ta da lita 20, 000 na man da ke matukar tsada da karanci a sassan Kano da ma Najeriya
  • Jami'an tsaro na zurfafa bincike domin gano karin bayanai kan safarar man kafin daukar matakin shari'a a kan masu laifin, duk da yanzu an mayar da man inda aka dauko shi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Hukumar tsaron farar hula ta NSCDC ta tabbatar da kama wata tankar mai da ake kokarin karkatarwa daga jihar Kano zuwa Katsina.

Kara karanta wannan

Wata mahaifiya ta kashe danta mai shekara 1 a jihar Delta

A sakon da jami'in hulda da jama'a na hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi ya aikewa Legit Hausa, an gano tankar na dauke da litar mai dubu ashirin.

An kama tankar man ne a titin Ibrahim Taiwo a Kano
Hukumar NSCDC ta mayar da litar fetur 20, 000 gidajen mai yayin da ake ci gaba da bincike Hoto: UGC Ibrahim Idris Abdullahi
Asali: UGC

Ya ce kwarya-kwaryar bincikensu ya gano cewa asalin man an turo shi ne zuwa gidajen man da ke Kano, amma aka samu wasu bata-gari na kokarin fitar da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ana binciken masu safarar fetur," NSCDC

Hukumar tsaron farar hula ta NSCDC a Kano ta ce ta fara binciken wadanda ake zargi da kokarin safarar tankar mai daga jihar Kano zuwa Katsina.

Kakakin hukumar, Ibrahim Idris Abdullahi ne ya tabbatar da hakan kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Ya ce an kama tankar man ne a titin Ibrahim Taiwo road ta na kokarin fita zuwa wasu sassan Katsina.

Kakakin ya ce za a mayar da fetur din zuwa gidan man da aka dauko saboda da su domin ci gaba da sayarwa jama'a.

Kara karanta wannan

Fadan daba: fusatattun matasa sun cinnawa kasuwa wuta a Lagos

Ibrahim Idris Abdullahi ya ce ba za su yi kasa a gwiwa na wajen hukunta wadanda aka kama da zarar sun kammala bincike, kamar yadda Stallion Times ta wallafa.

An harbe matashi a layin man fetur

A wani rahoton kun ji an shiga rudani bayan wani jami'in tsaro ya harbe wani matashi mai suna Toheeb Eniasa a layin shan mai a Ikoyi da ke jihar Legas.

Rahotanni sun ce jami'an tsaron sun yi kokarin shiga gaban mutane su sha mai, lamarin da ya sa al'umma su ka nuna rashin amincewarsu har ta kai ga harbe matashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel