Katsina: Yadda magidanci ya kashe amaryarsa ya jefa gawarta a rijiya
Wani magidanci mai shekara arba'in, Abdulrahaman Abdulkarim ya shiga hannun 'yan sanda a jihar Katsina saboda zarginsa da ake yi da kashe matarsa da jefa gawarta a cikin rijiya.
Ana zargin Abdulkarim ya aikata laifin ne a kauyen Madabu -Dabawa da ke karamar hukumar Dutsinma na jihar kamar yadda The punch ta ruwaito.
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Alhamis.
Ya ce wadda aka kashe, Wasila Sara, mai shekara 19, amaryar Abdulkarim ce.
DUBA WANNAN: Hamshakin biloniyan Najeriya ya shirya angwancewa da diyar Trump
Kakakin 'yan sandan ya ce, "A ranar 14/06/2020 misalin karfe 2 na rana mun samu rahoto cewa wani Abdulrahaman Abdulkarim mai shekara 40 a kauyen Madabu, Dabawa, karamar hukumar Dutsinma na jihar Katsina ya kashe amaryarsa wata Wasila Sada mai shekaru 19 kuma ya jefa gawarta a rijiya.
"Daga nan, DPO na Dutsinma ya jagoranci jami'an zuwa inda abin ya faru, sun gano gawar sun kuma kai ta babban asibiti inda aka tabbatar ta mutu bayan gwaje gwaje da likita ya yi.
"An kama wanda ake zargi da aikata laifin kuma yana taimakawa yan sanda wurin bincike. A halin yanzu ana cigaba da gudanar da bincike."
A wani labarin, kun ji cewa 'yan bindiga a yammacin ranar Talata sun kai hari kauyen Karare da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina inda suka sace diyar dagajin kauyen, Ciroma Ahmadu Karare.
Mazauna kauyen sun ce 'yan bindigan sun sace matashiyar mai shekaru 20 tare da wata mata mai shekara 23 da ke da goyo a bayanta a lokaci da aka yi awon gaba da su kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Yan bindigan da aka ce adadinsu ya kai 20 sun isa kauyen ne a kan babura dauke da bindigu kamar yadda suka saba.
Rahotanni sun ce sun bi gidaje da dama suna yi wa mutane fashi ciki har da gidan dagajin kauyen inda suka sace diyarsa.
Daya daga cikin mazauna kauyen, Mustapha Ruma ya ce yan bindigan sun kwace wayar dagajin kauyen sannan suka ba shi sabon layin waya.
Sun umurci ya kira su domin tattauna abinda zai biya domin fansar diyarsa. Yan bindigan kuma sun sace wasu dabobi da kayan abinci daga wurin mazauna kauyen yayin harin.
Da aka tuntube shi a wayar tarho, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce "har yanzu ina bincike a kan lamarin".
Bai kira ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aika masa ba har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng