Fatima Alkali: Ɗalibar da Ta Rikita Arewa Bayan Ta Yi Kacal Kaca da Jarabawar UTME

Fatima Alkali: Ɗalibar da Ta Rikita Arewa Bayan Ta Yi Kacal Kaca da Jarabawar UTME

  • Yayin da hukumar JAMB ta sake sakamakon jarrabawar UTME, wata daliba 'yar Arewa ta burge 'yan Najeriya
  • Dalibar mai suna Fatima Saleh Alkali ta samu maki 336 a jarrabawar da aka gudanar wanda mafi yawa suka fadi
  • Wannan na zuwa ne bayan sake sakamakon inda hukumar ta ce 76% daga cikin daliban sun samu maki kasa da 200

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Yobe - Wata daliba mai suna Fatima Saleh Alkali ta burge mutanan Najeriya bayan fitar da sakamakon jarrabawar UTME a bana.

Fatima ta samu maki 336 a jarrabawar ta bana duk da yawan faduwa da aka samu daga ɗalibai.

Daliba daga Arewa ta yi fice bayan samun mako 366 a jarrabawar UTME
Fatima Alkali daga jihar Yobe ta samu maki 366 a jarrabawar UTME. Hoto: @yakubwudil.
Asali: Twitter

Wane kira ya yi ga gwamnan Yobe?

Kara karanta wannan

"Ya kware a cin amana": APC ta ja kunnen Tinubu kan sake jiki da gwamnan PDP

Wani mai amfani da kafar X, Dakta Yakubu Sani Wadil shi ya wallafa haka a yau Alhamis 2 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wudil ya ce ya kamata a yi kira ga Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bata tallafin karatu har zuwa matakin digirin-digirgir.

Ya ce tabbas za ta daga darajar jihar a idon duniya idan aka mara mata baya wurin ɗaukar nauyin karatunta.

Yawan maki da Fatima ta samu a UTME

Dalibar ta samu maki 68 a Turanci sai kuma 93 a darasin lissafi da maki 87 a Physics sai kuma 88 a Chemistry.

"Wannar daliba ce daga Arewacin Najeriya, Fatima Saleh Alkali, ta samu maki 366 a jarrabawar UTME duk da yawan faduwa da aka yi."
"Ya kamata mu hada hannu domin yin kira ga gwamnan jihar Yobe ya dauki nauyin karatunta har matakin PhD, za ta daga sunan jihar Yobe idan aka ɗauki nauyinta yadda ya kamata."

Kara karanta wannan

JAMB 2024: Hazikin dalibi dan shekara 18 ya samu maki 313 a jarabawar UTME

- Dakta Yakubu Wudil

Wannan na zuwa ne bayan hukumar JAMB ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME na wanna shekara.

Matashi ya samu maki 313 a JAMB

Kun ji cewa Bayan samun maki 313 a jarrabawar shiga manyan makarantu (UTME), dan shekaru 18, Ebeniro Akachi, ya tabbatarwa duniya cewa ana yin nasara idan aka yi aiki tukuru.

Akachi ya yi nasarar samun maki 313 daga darusa hudu da ya amsa tambayoyi a kansu a jarabawar da ya zana a karo na biyu.

Dalibin, wanda ya kammala karatunsa a kwalejin gwamnatin tarayya da ke Okigwe a jihar Imo ya ci 248 a jarabawarsa ta farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.