Hajjn 2024: Hukumar NAHCON Ta Fadi Ranar da Jirgin Farko Na Alhazai Zai Tashi
- Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta ce alhazan Nijeriya za su fara yin kwanaki hudu a Madina kafin a fara aikin Hajji
- Hukumar ta kuma bayyana cewa za a fara jigilar alhazan daga ranar 15 ga Mayu, 2024 daga filayen jirgin sama 10 da aka zaba
- Shugaban NAHCON, Malam Jalal Arabi ne ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki na harkar Hajji da Umrah a Abuja
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta ce a ranar 15 ga Mayu, 2024 ne za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
Shugaban hukumar NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi ne ya bayyana haka a jawabinsa na bude taron masu ruwa da tsaki na harkar Hajji da Umrah na da aka gudanar a Abuja.
Tsare-tsaren aikin Hajjin bana
Arabi ya ce maniyyara 65,500 ne za su halarci aikin Hajjin shekarar 2024, yana mai cewa za ayi jigilar su daga filayen jiragen sama 10 na kasar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban NAHCON ya ce hukumar ta yanke shawarar cewa a aikin Hajjin bana, dukkanin alhazan Nijeriya za su fara yin kwanaki akalla hudu a Madina kafin a fara aikin Hajjin.
Da yake jawabi a wajen taron, Arabi ya ce haduwar masu ruwa da tsaki wani nauyi ne da Allah ya rataya a kan kowa, yana mai cewa an yi dogon nazari kafin a zabi taken taron.
Tattaunawa da masu ruwa da tsaki
Jaridar Leadership ta rahoto taken taron masu ruwa da tsakin shi ne: "Haɗin kai, taimakekeniya da yin aiki tare: Nasarar gudanar da ayyukan Hajji na 2024"
Ya ce hukumar alhazan ta ga ya dace ta tattauna da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara.
Ya kara da cewa yana da kyau duk masu ruwa da tsaki su hada kai domin alhazai su samu gogewar aikin hajji a bana.
NAHCON ta kara kudin aikin Hajji
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar NAHCON ta sanar da karin kudin zuwa aikin Hajjin 2024 ga alhazan Najeriya.
Hukumar wacce ta ce karin kudin ya zama dole ne saboda tashin dala ta bayyana cewa maniyyata za su biya karin Naira 1,918,032.91.
Asali: Legit.ng