"Ba Talakawa Kadai Ba Ne", Dangote Ya Koka Kan Illar da Karyewar Naira Ya Yi Masa

"Ba Talakawa Kadai Ba Ne", Dangote Ya Koka Kan Illar da Karyewar Naira Ya Yi Masa

  • Yayin da talakawa ke kokawa kan faduwar darajar Naira, Alhaji Aliko Dangote ya koka kan Illar da hakan ya yi masa
  • Dangote ya ce babbar matsalar da ya kawo musu cikas a kanfaninoninsa a 2023 bai wuce karyewar darajar Naira ba
  • Attajirin ya bayyana cewa hakan ya yi matukar tasiri wurin samun kudin shiga inda ya ce za su shawo kan matsalar ba da jimawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Attajirin Nahiyar Afirka, Aliko Dangote ya koka kan faduwar darajar Naira a Najeriya.

Attajirin ya ce faduwar darajar Naira shi ne mafi munin masifa da kamfanoninsa suka fuskanta a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Lantarki: Minista ya fadi masifar da za a shiga idan ba a kara kudi ba, ya yi gargadi

Dangote ya koka kan illar faduwar Naira ga kamfanoninsa
Aliko Dangote ya magantu kan masifar da suka shiga bayan faduwar darajar Naira a Najeriya. Hoto: Dangote Industries.
Asali: Facebook

Wane hali kamfanonin Dangote suka shiga?

Dangote ya bayyana haka ne yayin babban taron shekara-shekara da kamfanin sukari ya gudanar, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kamfanoni da dama a Najeriya sun shiga wani hali wanda ke hana su biyan kudi ga masu hannun jari a shekarar.

Har ila yau, ya ce shekarar ta zo da kalubale kasancewar an gudanar da zabe da kuma rantsar da sabuwar gwamnati, TheCable ta tattaro.

Dangote ya koka kan faduwar darajar Naira

"Muna iya bakin kokari domin ganin mun shawo kan matsalar da kuma biyan masu hannun jari."
"Babbar matsalar da aka samu shi ne faduwar darajar Naira daga N460 zuwa N1,400 wanda ya shafi kamfanoninmu."
"Idan ka duba za ka ga kusan 97% na kamfanoni musamman na abinci ba za su iya biyan masu hannu jari ba a wannan shekara, amma za mu yi kokarin kawo karshen matsalar ba da jimawa ba."

Kara karanta wannan

Dillalan mai sun fadi lokacin da wahalar fetur da ta mamaye Najeriya za ta kare

- Aliko Dangote

Dangote ya fadi hanyar rage farashin kaya

A wani labarin, mun ruwaito muku cewa attajiri Aliko Dangote ya bayyana hanyar da za a bi wurin tabbatar da farashin kaya ya sauka a Najeriya.

Dangote ya ce hanya mafi sauki na rage hauhawan farashin kaya shi ne rage farashin man dizal a kasar baki daya.

Attajirin ya bayyana haka ne bayan rage farashin dizal a matatarsa daga N1,200 zuw 1,000 a kwanakin baya domin saukakawa al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.