Jerin Gwamnonin da Suka Kara Albashi Ga Ma'aikata a Jihohinsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Wasu gwamnonin jihohin Najeriya sun ƙara albashin ma'aikatan gwamnati a jihohinsu saboda tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar nan.
Ma’aikatan gwamnati a faɗin ƙasar nan sun yi ta kokawa domin samun ƙarin albashi saboda halin da tattalin ƙasar nan ya tsinci kansa a ciki.
Wasu daga cikin ma'aikatan kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu inda aka yi musu ƙarin albashi.
Gwamnonin da suka ƙara albashin ma'aikata
Ga jerin sunayen gwamnonin jihohin Najeriya da suka amsa kiran ma’aikata tare da ƙara musu albashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Gwamna Godwin Obaseki na Edo
Na farko a jerin sunayen shine Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo. Obaseki ya sanar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan jihar a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu.
Sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan jihar Edo ƙari ne daga N40,000 zuwa N70,000, cewar rahoton jaridar The Nation.
Gwamnan na jam’iyyar PDP ya ce a ranar Laraba 1 ga watan Mayu, 2024 ne ake sa ran za a fara biyan mafi ƙarancin albashin.
2. Gwamna Bassey Otu na Kuros Ribas
Gwamna Bassey Otu ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi na N40,000 ga ma’aikatan gwamnati a jihar Kuros Ribas.
Gwamnan na jam’iyyar APC ya ce sabon tsarin albashin ya yi dai-dai da abin da jihar za ta iya biya, duba da yanayin kason da take samu daga gwamnatin tarayya, cewar rahoton jaridar Leadership.
Gwamna Bassey Otu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko wajen biyan albashi da kuɗaɗen fansho na ma’aikata.
3. Gwamna Francis Nwifuru na Ebonyi
Wani gwamnan APC da ya yi wa ma’aikatan gwamnati ƙarin albashi a jiharsa shi ne Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi.
Wannan ci gaban ya zo ne watanni takwas bayan gwamnan ya ƙara Naira 10,000 ga albashin ma’aikatan jihar Ebonyi a watan Yulin 2023.
Hakan dai ya kasance cika alƙawarin da gwamnan ya yi na ba da fifiko ga jin daɗin ma’aikatan jihar tare da ƙara haɓɓaka ayyukan ma’aikata.
Lokaci fara aikin sabon albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata a Najeriya zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayun 2024.
Gwamnatin ta ce ta yanke wannan hukuncin duk da cewa kwamitin da ke da alhakin ba da shawara kan ƙarin albashin ma'aikata bai gabatar da rahotansa ba.
Asali: Legit.ng