Gwamnatin Kwara ta yi Kyautar Tsala-tsalan Motoci ga Alkalai 12
- Gwamnatin jihar Kwara ta raba tsala-tsalan motocin zamani ga alkalai 11 a jihar domin su ji dadin gudanar da aiki
- Shi kuwa alkalin-alkalan jihar, Abiodun Adebara dalleliyar mota kirar 2024 Toyota Land Cruiser gwamnati ta ba ofishinsa
- Ana sa ran gwamnatin za ta karo wasu motocin domin rabawa ga manyan alkalan da ke aiki a manyan kotunan jihar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kwara, Ilorin-Gwamnatin jihar Kwar ta yi kyautar kasaitattun motoci kirar Toyota Fortuner Jeeps 11 ga alkalan jihar domin kyautata musu, da kara musu kwarin gwiwar cigaba da ayyukansu cikin nishadi.
Rahotanni sun ce shi kuma alkalin-alkalan jihar, Abiodun Adebara gwamnatin ta gwangwaje ofishinsa da mota kirar 2024 Toyota Land Cruiser.
A wani labari da gwamnatin jihar ta Kwara ta wallafa a shafinta na Facebook, alkalin-alkalan ya ce ko a watan Fabarairun bana, sai da gwamnatin ta yi wa alkali manyan kotuna biyar a jihar kyautar motocin alfarma kirar Toyota Fortuner.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an samu kudin sayen motocin ne a cikin kudin kasafin da aka ware musu tun da farko a shekarar 2023.
Gwamnati za ta raba wasu motocin
Gwamnatin jihar Kwara karkashin jagorancin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq za ta karawa wasu alkalan jihar sabbin motocin alfarma.
Alkalin-alkalan jihar, ya tabbatar da hakan, inda ya bayyana cewa alkalai biyar ne za su samu kyautar motocin, kamar yadda Leadership News ta wallafa.
Ya kara da cewa dama ya kamata tun da fari a bawa dukkanin manyan alkalan da aka nada ababen hawa, kamar yadda ya ke a dokokin hukumar kula da harkokin Shari'a (NJC).
Abiodun ya gode wa gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da ya ga dacewar kula da walwalar alkalan da ke aiki a jiharsa.
Sanata Barau ya raba motoci 60
A baya kun ji yadda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin ya raba motoci guda sittin ga al'ummar Kano domin dogaro da kai.
Ofishin mataimakin shugaban majalisar ya bayyana cewa an zabo wadanda su ka ci gajiyar motocin ne daga sassa daban-daban na rayuwa kama daga yan siyasa zuwa manoma.
Asali: Legit.ng