Gwamnan APC Ya Tuna da Ma'aikata Bayan Ya Yi Musu Karin N10,000 a Albashinsu
- Ma’aikatan jihar Ebonyi sun samu kyautar kuɗi domin murnar zagayowar ranar ma’aikata ta duniya a ranar Laraba, 1 ga watan Mayun 2024
- Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Francis Nwifuru ta tabbatar da hakan a ranar Laraba a filin wasa na Pa Oruta Ngele da ke Abakaliki, babban birnin jihar
- Wannan dai shi ne karo na biyu da ma'aikatan Ebonyi ke samun ƙarin albashi cikin kasa da shekara ɗaya ta gwamnatin Francis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifiru a ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, ya yi ƙarin Naira 10,000 ga albashin ma’aikatan jihar.
Gwamna Francis Nwifuru ya sanar da ƙarin albashin ne ga ma'aikata a wajen bikin ranar ma'aikata ta shekarar 2024 da aka gudanar a jihar.
Kamar yadda tashar Channels tv ta ruwaito, an gudanar da bikin ne a filin wasa na Pa Oruta Ngele da ke Abakaliki, babban birnin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya yi ƙarin albashi a baya
Idan dai za a iya tunawa a watan Yulin 2023, kusan wata ɗaya a kan karagar mulki, Gwamna Francis ya ƙara Naira 10,000 ga albashin ma’aikatan jihar Ebonyi tare da bayyana cewa zai ba da fifiko ga jin daɗin ma’aikatan jihar.
A jawabinsa na ranar Laraba domin bikin ranar ma’aikata ta shekarar 2024, Gwamna Francis Nwifuru ya jaddada cewa ma’aikatan gwamnati za su ci gaba da kasancewa abokan hulɗa domin samun ci gaba, inji rahoton The Punch.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙara inganta danganta mai kyau tsakaninta da ma'aikata domin ƙara musu ƙwarfin gwiwa wajen kawo ci gaba mai ɗorewa a jihar.
Ƙarin N10,000 ya sanya ma'aikatan jihar sun samu ƙarin N20,000 a albashinsu tun bayan hawan gwamnan kan karagar mulki.
Ƙarin albashin gwamnatin tarayya
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta sanar da yin ƙarin albashi ga ma'aikata da kaso 25% zuwa 35%.
Ma'aikatan da gwamnatin ta yi wa ƙarin albashi sun haɗa da masu karɓar albashi na bai-ɗaya na CONPSS, CONRAISS, CONPOSS, CONPASS, CONICCS da CONAFSS.
Asali: Legit.ng