Gwamnan APC Ya Zama Na 2 Wurin Kara Mafi Karancin Albashi Ga Ma'aikata, Ya Ba Su Hakuri

Gwamnan APC Ya Zama Na 2 Wurin Kara Mafi Karancin Albashi Ga Ma'aikata, Ya Ba Su Hakuri

  • Yayin da ake bikin ranar ma'aikata a Najeriya, gwamnan jihar Kuros Riba ya amince da sabon mafi karancin albashi
  • Gwamna Bassey Otu ya amince da biyan N40,000 ga ma'aikatan jihar inda ya ce sun yi karin ne duba da halin da jihar ke ciki
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wasu ma'aikatan jihar Gombe kan karin albashi da wasu jihohi ke yi a ranar ma'aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Cross River - Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Riba ya amince da karin mafi karancin albashi ga ma'aikata jiharsa.

Bassey Otu ya amince da biyan N40,000 ga ma'aikatan jihar Kuros Riba inda ya ce ya yi hakan ne duba da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta koka kan yadda Borno ke biyan 'yan fansho N4,000 a wata

Gwamnan PDP ya kara mafi karancin albashi ga ma'aikata
Gwamna Bassey Otu na Kuros Riba ya amince da N40,000 a matsayin mafi karancin albashi. Hoto: Bassey Otu.
Asali: Facebook

Albashi: Wane alkawari Gwamna Otu ya yi?

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin bikin ranar ma'aikata a yau Laraba 1 ga watan Mayu a birnin Calabar, Cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba ba ma'aikata kulawa na musamman wurin biyan albashi da fansho da kuma sauran hakkokinsu.

"Jihar Kuros Riba ta na fama rashin samun isassun kuɗi daga Gwamnatin Tarayya da kuma tulin bashi."
"Mun amince da ƙarin kudin tallafin ne duba da yanayi ba wai son ranmu ba."

- Bassey Otu

Gwamna Otu ya ba ma'aikata hakuri

A bangaren biyan giratuti da sauran hakkokin ma'aikata, gwamnan ya roki al'umma da su yi hakuri inda ya ce yana kokarin shawo kan matsalar.

Gwamna Otu ya ba ma'aikata tabbacin ci gaba da kulawa da walwalarsu ba tare da matsala ba, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Karin Albashi: Kungiyar TUC ta ba 'yan Najeriya tabbaci kan hauhawan farashin kaya, ta fadi dalilai

Ya bayyana babbar alaka da ke tsakanin gwamnati da ma'aikata inda ya ce sune sular ci gaban kowace Gwamnati.

Tattaunawar Legit Hausa da wasu ma'aikata

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu ma'aikatan jihar Gombe kan karin albashi da wasu jihohi ke yi.

Abdulkadir Umar ya ce ya kamata gwamnan Gombe ya yi duba ga halin da ake ciki domin karin mafi karancin albashi.

"A gaskiya ana cikin wani hali kuma babu wani alkawari na karin mafi karancin albashi a Gombe."

- Abdulkadir Umar

Har ila yau, Aliyu Muhammad wanda malamin makaranta ne ya ce:

"Mun ji kungiyar NLC ta na cewa har yanzu a Gombe ba a biyan mafi karancin albashi na N30,000, gaskiya wannan abin takaici ne ya kamata a sake zama."

Obaseki ya kara karancin albashi zuwa N70,000

A wani labarin, an ji Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jiharsa.

Obaseki ya tabbatar da cewa zai fara biyan N70,000 a matsayin mafi karancin albashi a jihar duba da yanayin da ake ciki a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel