Kwana 7: Kungiyoyin Kwadago sun Ba Gwamnati Wa'adin Janye Karin Kudin Wuta

Kwana 7: Kungiyoyin Kwadago sun Ba Gwamnati Wa'adin Janye Karin Kudin Wuta

  • Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun bawa gwamnatin tarayya mako guda ta janye karin kudin wutar lantarki da ta yi a watannin baya
  • Shugaban kungiyar kwadago, Joe Ajaero da shugaban kungiyar yan kasuwa, Festus Osifo su ka ba gwamnati wa'adin yau a birnin tarayya Abuja
  • Wannan na zuwa ne sa'ilin da ake bikin ranar ma'aikata a fadin duniya, sai dai ma'aikatan Najeriya na bikin ranar yayin da su ke naman karin albashi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da takwararta ta yan kasuwa (TUC) sun ba gwamnatin tarayya wa'adin kwanki bakwai da ta janye karin kudin wutar lantarkin da ta yi wa yan Najeriya.

Kara karanta wannan

1 ga watan Mayu: Gwamnati ta fadi ranar da sabon albashin ma'aikata zai fara aiki

Shugaban NLC, Mista Joe Ajaero, da Mista Festus Osifo na TUC ne su ka bukaci gwamnatin ta janye karin yayin bikin ranar ma'aikata da ya gudana yau a Abuja.

Kungiyar kwadago ta nuna bacin rai kan yadda yan Najeriya ke zaune cikin duhu
Kungiyoyin sun nemi gwamnati ta mayar da kudin wuta yadda ya ke a da Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

NLC, TUC da karin kudin lantarki

A rahoton da Vanguard News ta wallafa, shugabannin biyu sun nuna bacin ransu kan matsalar wutar da ake fuskanta a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana cewa daya daga matsalolin da ke barazana ga tattalin arzikin kasar nan shi ne rashin wuta duk kuwa da janyo yan kasuwa cikin sashen.

"Sam bai da ce ba a tilastawa 'yan Najeriya biyan kudin wutar da babu. Kudin wuta da ake tilastawa yan Najeriya su na biya kwace ne da tsakar rana,"

- NLC da TUC

Kungiyoyin sun nemi baza motoci

Shugabannin NLC da TUC, Joe Ajaero da Festus Osifo sun tunatar da gwamnati alkawarin da ta yi na samar da motocin CNG domin saukaka zirga-zirga da kuma rage gurbatar muhalli, kamar yadda Channels Television ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Ba zai tsinana komai ba', gamayyar 'yan siyasa sun soki Tinubu a ranar ma'aikata

A makon da ya gaba ne fadar shugaban kasa ta ce za ta samar da motoci 2700 masu amfani da CNG; wani nau'i na makamashi mara gurbata muhalli.

Kungiyoyin na ganin samar da motocin zai taimakawa ma'aikatan kasar nan matuka.

Yan siyasa sun caccaki gwamnati

Gamayyar kungiyar jam'iyyun siyasa a Najeriya (CUPP) ta ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai tsinanawa yan kasar nan komai ba.

Kwamared Mark Adebayo, shi ne sakataren kungiyar, ya kuma ce suna bakin cikin halin kuncin da yan kasar nan ke ciki a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.