Dalibai Sun Rasu a Hatsarin Jirgin Ruwa a Kano, an Ceto 1 da Rai

Dalibai Sun Rasu a Hatsarin Jirgin Ruwa a Kano, an Ceto 1 da Rai

  • Akalla daliban Kwalejin Aikin Gona ta Audu Bako da ke kusa da Danbatta guda biyu sun mutu a hatsarin kwale-kwale a tafkin Thomas
  • Jami’in yada labarai na karamar hukumar Makoda, Sani Muhammadu ya ce an gano gawar daya daga cikin daliban, Abubakar Sanusi
  • Yayin da dalibi daya da matukin jirgin suka tsallake rijiya ta baya-baya, Muhammadu ya ce ana ci gaba aikin ceto domin gano dayan dalibin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Makoda, jihar Kano - Ana fargabar cewa dalibai biyu na Kwalejin Aikin Gona ta Audu Bako da ke kusa da Danbatta sun mutu bayan kwale-kwalen da suka hau ya kife.

An ruwaito cewa kwale-kwalen ya kife a tsakiyar tafkin Thomas da ke karamar hukumar Makoda a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Lamari ya lalace; Gwamantin jihar Kano ta saka dokar ta baci a kan harkar ilimi

Jirgin ruwa ya kife da dalibai a Kano, 2 sun mutu yayin da ake neman wasu
Wasu dalibai guda 2 sun hallaka a hatsarin jirgin ruwa a Kano.
Asali: Twitter

Sai dai an ceto daya daga cikin daliban, Abubakar Salisu, yayin da ake ci gaba da neman sauran daliban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ceto direban jirgin ruwa da dalibi

Jami’in yada labarai na karamar hukumar Makoda, Sani Muhammadu ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Talata a lokacin da daliban ke komawa kwalejin.

Ya ce aikin ceto ya kai ga gano gawar daya daga cikin daliban, Abubakar Sanusi.

Muhammadu ya ce ba a gano dayan dalibin mai suna Ado Salisu ba a lokacin da aka dakatar da aikin ceton.

Amma jami'in ya tabbatar da cewa ma’aikatan ceto za su koma bakin aiki da safiyar yau (Laraba).

A cewarsa, direban kwale-kwalen, Hassan Haruna ya tsallake rijiya da baya, rahoton jaridar Daily Trust.

Yawaitar hatsarin jirgin ruwa a Najeriya

Wani mazaunin Danbatta Abba Muhammad ya kara da cewa dalibin da aka ceto yana karbar magani a babban asibitin Danbatta.

Kara karanta wannan

Dillalan mai sun fadi lokacin da wahalar fetur da ta mamaye Najeriya za ta kare

Wannan tafkin na Thomas da iftila'in ya faru a cikinsa yana da tazarar kilomita biyar daga makarantar.

Wannan lamari dai ya yi karin haske kan yadda ake yawan samun hatsarin kwale-kwale a Najeriya, wanda galibi ana alakanta shi da amfani da jiragen ruwa da suka tsufa da kuma rashin bin ka’idojin da suka dace.

An kama dillalin wiwi a Kano

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama daya daga cikin rikakkun masu dillancin miyagun kwayoyi musamma tabar wiwi.

Haruna Kiyawa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya ce an kama 'Badoo' ne a wani samame a yankin Tukuntawa inda ya ke safarar kwayoyi ga matasa da matan aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.