Ganduje vs Abba: Kwamiti Ya Bukaci Kanawa Su Kawo Bayanan da Za Su Taimaka

Ganduje vs Abba: Kwamiti Ya Bukaci Kanawa Su Kawo Bayanan da Za Su Taimaka

  • Kwamitin da ke bicike kan zargin Abdullahi Ganduje da rashawa ya nemi taimakon jama'a da bayanai na musamman a kan akin da yake
  • Shugaban kwamitin ne, mai shari'a Farouk Adamu, ya bayyana haka a lokacin zamansu na yau Litinin, 29 ga watan Afrilu
  • Ya kuma kara bada sanarwa a kan lokacin da za su fara zama na musamman domin sauraron kara da yanke hukunce-hukunce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

A yayin sauraren korafin da gwamnatin Kano ta kai shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, kwamitin ya bukaci al'umma su taimaka da bayanai na musamman.

ganduje
Kwamitin bincike ya bukaci shaidu kan zargin da ake wa Ganduje. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Kwamitin ya nemi taimakon ne domin samun cikakkun bayanai da za su taimaka wurin yin adalci cikin shari'ar da zai gabatar nan gaba.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah a Kano ta yi ram da kwamishina kan zargin lalata da matar aure

Kiran kwamitin Ganduje ga al'umma

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa mai Shari'a Farouk Adamu ne ya bukaci al'umma da su taimaka da bayanai a zaman kwamitin na yau Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce duk wanda yake da wani bayani da zai taimaka musu zai iya rubutawa ya mika a sakateriyar Audu Bako, cewar jaridar Daily Nigerian

Kwamitin ya kuma jaddada cewa zai yi adalci a cikin hukuncin da zai yanke tsakanin Ganduje da gwamnatin jihar.

Ya ake ciki kan binciken Ganduje?

Mai Shari'a Farouk ya kara da cewa yanzu haka suna matakin neman gaskiya ne a kan abin da ya faru kuma sun ba gwamnatin sharawa kan matakan da ya kamata ta dauka.

Ya kara da cewa korafin da gwmantin ta shigar ya shafi kadarorin gwamnati da ake zargin Ganduje da sacewa.

Ya kuma ce za su tuntubi dukkan waɗanda aka yi haɗaka da su wajen salwantar kadarorin domin sanin hakikanin abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Gwamna a Arewa ya kafa kwamitin kayyade farashin kaya

A karshe ya ce za su sanar da ranar da za a fara sauraron karar gadan-gadan ta kafafen yada labarai.

Kotu ta daga shari'ar Ganduje

A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun jihar Kano ta dage sauraron shari'ar tuhumar rashawa da ake yi wa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Kotun ta sanya ranar 16 ga watan Mayu, 2024 matsayin ranar da za ta yi hukunci kan bukatar mika takardar sammaci, ba gaba da gaba ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng