Hukumar Shirya Jarabawa JAMB Ta Saki Sakamakon Jarabawar UTME 2024
- Sakamakon jarabawar share fagen shiga manyan makarantun gaba da sakandire (UTME) wanda ɗalibai suka kammala ya fita
- Hukumar da ke da alhakin shirya jarabawar (JAMB) ce ta bayyana sakin sakamakon ɗalibai miliyan 1.94 da suka zana jarabawar a bana 2024
- Shugaban JAMB na ƙasa, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya sanar da haka yayin hira da ƴan jarida a hedkwatar JAMB da ke Bwari a Abuja
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar da ke shirya jarabawar share fagen shiga manyan makarantu (JAMB) ta saki sakamakon dukkan ɗaliban da suka zauna jarabawar a 2024.
Shugaban JAMB na ƙasa, Farfesa Ishaq Oloyede, ne sanar da sakin sakamakon jarabawar UTME a taron manema labarai a hedkwatar JAMB da ke Bwari a Abuja.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa an fara zana jarabawar ne a ranar Jumu'a, 19 ga watan Afrilu kuma an kammala a ranar Litinin 29 ga watan Afrilu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka samu jinkirin JAMB?
A cewar rahoton Punch, JAMB ta yi jinkirin sakin sakamakon jarabawar ne domin ƙara nazari da bincike da tsefe sakamakon don kar a samu matsala.
Hukumar ta yanke shawarin ƙara kwanaki kafin fitar da sakamakon jarabawar domin tabbatar da gaskiya game da zargin wani ya zana ma wani da sauran laifuffukan satar amsa.
Legit.ng ta rahoto cewa Oloyede ya ce sama da ɗalibai miliyan 1.94 ne suka yi rajista tare da zana jarabawar UTME a 2024 a garuruwa 118 da cibiyoyi sama da 700 a fadin kasar.
Farfesa Oloyede ya ce jarabawar ta yi sauri saboda hukumar ta yi ƙoƙarin kawar da duk wata matsala wajen tantance yatsan kowane ɗalibi ba tare da tangarda ba.
Tun farko dai JAMB ta nuna cewa za ta saki sakamakon jarabawar a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu, 2024.
Obaseki ya ƙara mafi karancin albashi
A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin da za a riƙa biyan ma'aikata a jihar.
A wurin kaddamar da sabon ofishin kwadago a jihar Edo, gwamnan ya ce sabon mafi ƙarancin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu, 2024.
Asali: Legit.ng