'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Matafiya Wuta, Sun Tafka Ɓarna a Titin Abuja Kaduna

'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Matafiya Wuta, Sun Tafka Ɓarna a Titin Abuja Kaduna

  • Ƴan bindiga sun kai sabon hari kan matafiya a titin Kaduna zuwa Abuja, sun kashe direban mota, sun ɗauki mutum biyu
  • Wani mazaunin Jere, Yahuza Alhassan, ya bayyana cewa direban da aka kashe yana hanyar komawa gida daga kasuwa lamarin ya faru
  • An tattaro cewa a makon jiya ƴan bindiga sun buɗe wa wata motar bas wuta, suka tafi da fasinjojin gaba ɗaya zuwa cikin daji

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun sake komawa kan babban titin nan da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja, inda suka kashe mutum ɗaya a sabon harin da suka kai.

Miyagun ƴan ta'adda sun harbe direba mai suna Danladi Jobe har lahira tare da yin garkuwa da wasu mutane biyu a titin Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari a wurin zaman makoki, sun kashe bayin Allah

IGP Kayode.
Yan bindiga sun kashe direba, sun ɗauki mutum biyu a titin Abuja-Kaduna Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Wani mazaunin Jere, Yahuza Alhassan, ya shaida wa wakilin Daily Trust ta wayar tarho ranar Litinin cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:33 na dare a Dogon-Fili, mai tazarar kilomita kadan da garin Jere.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa mamacin na kan hanyarsa ta dawowa daga kasuwar wani ƙauye da ke kusa, kwatsam ƴan bindigar suka farmaki motarsa.

Ƴan bindigar sun fito ne daga cikin jeji kuma suka buɗe wa motar wuta kan mai uwa da wabi, nan take suka yi ajalin direban.

Ƴan bindiga sun ƙwace makudan kuɗi

Alhassan ya faɗi sunan ɗaya daga cikin waɗanda maharan suka sace watau Shu'aibu, wanda ya ce manomi ne a yankin.

A cewarsa, ƴan bindigar sun kwace kudi kusan Naira miliyan ɗaya daga hannun Shu'aibu.

"Bayan sun kashe direban sai suka bi mutumin, wanda manomi ne kuma suka kwace masa kudi Naira 980,000, kafin daga bisani su tafi da shi tare da wani mutum daya na cikin motar zuwa cikin daji,” inji shi.

Kara karanta wannan

An kama mutum 2 yayin da wani gini mai bene ya kashe mutane a jihar Kano

Abin da ya faru makon jiya

An tattaro cewa makamancin haka ta faru a makon da ya gabata inda wasu ‘yan bindiga suka bude wuta kan wata motar bas Hiace a kusa da Gadan-Malam a titin Abuja-Kaduna.

Yayin wannan hari, ƴan bindigar sun yi awon gaba da gaba ɗaya fasinjojin da ke cikin motar, rahoton Leadership.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, bai amsa kiran waya ko saƙon tes da aka aike masa kan lamarin ba.

Yan bindiga sun kashe rayuka

A wani rahoton kuma yan bindiga sun kashe mutum huɗu yayin da suka kai farmaki wurin zaman makoki a jihar Enugu ranar Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan, wadanda ake zargin fulani makiyaya ne sun sun kai harin ne ba zato ba tsammani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel