Gwamnatin Najeriya Ta Fadi Hukuncin Wanda Aka Kama Yayi Kaciyar Mata
- Hukumar yaki da safarar mutane ta kasa ta bayyana hukuncin da zai shafi duk wanda ya yiwa mata kaciya a Najeriya
- Ta kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su isar da sakon ga dukkan wadanda bai riskesu ba domin kaucewa aikata laifin
- Bayanan na NAPTIP ya biyo bayan tambaya ce da wani mai amfani da kafar sada zumunta ya mata a kafar X ranar Lahadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP) ta bayyana hukuncin da zai faru da wanda ya yiwa mata kaciya.
Hukumar ta bayyana cewa akwai matakan dokar kasa daban-daban a kan wanda ya yiwa mata kaciya da wanda ya yi niyyar musu ba tare da ya zartar ba.
Hukuncin yiwa mata kaciya a Najeriya
A wata amsa da hukumar ta bayar a shafinta na X, ta ce duk wanda aka kama da laifin yi wa mata kaciya zai sha daurin shekaru hudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanda kuma aka kama da laifin yunkurin yin kaciyar zai sha daurin shekaru biyu a gidan gyaran hali
A cewar hukumar dokokin da suka tanadi hukuncin suna karkashin dokokin kasa da suka hana cin zarafin al'umma ne.
Sababin karin haske NAPTIP kan kaciyar mata
Bayanan da hukumar ta yi ya biyo bayan tambaya ne da wani mai amfani da shafin X, ya mata a ranar Lahadi da ta wuce.
Mutumin ya tambayi hukumar hukuncin yi wa mata kaciya a dokar Najeriya. Ga cikakkiyar amsar da NAPTIP ta bayar:
"Yi wa mata kaciya laifi ne a dokar kasa a karkashin dokar da ta hana cin zarafin al'umma ta shekarar 2015."
"Duk wanda aka kama da laifin zai sha daurin shekaru hudu, wanda kuma ya kudiri niyyar aikatawa zai sha daurin shekaru biyu."
"Muna kira ga gareku da ku isar da sakon ga sauran 'yan Najeriya cewa hukuncin yi wa mata kaciya laifi ne a dokar Najeriya."
- NAPTIP
NAPTIP ta kama mata mai satar yara
A wani rahoton, kun ji cewa jami’an NAPTIP sun yi nasarar kama wata mata wanda aka samu da kananan yara rututu da ake zargin sato su aka yi.
Wadannan yara sun koma hannun marikansu yayin da hukumar ta NAPTIP take bakin kokari wajen hana yin safarar mutane Najeriya.
Asali: Legit.ng