Kurungus! Ta yi masa kaciya, bayan yayi mata fyaɗe

Kurungus! Ta yi masa kaciya, bayan yayi mata fyaɗe

- Wani gardi ya fara zaman kurkuku yayin da asirinsa ya tonu a Katsina

- Wannan gardi dai ya samu nakasu ne a gabansa lokacin da wata yarinya tayi masa kaciya

Wani lamari mai ban ta’ajibi ya wakana a wata kotun jihar Katsina inda aka gurfanar da wani kato mai shekaru 30 sakamakon yarinyar da ake zargi yayi ma fyade ta yanke masa al’aura.

Kaakakin rundunar yansandan jihar, DSP Isa Gambo ne ya shaida ma kamfanin labarai na BBC Hausa, inda yace an kama mutumin ne a lokacin daya je neman samun shaidu daga wajen yansanda, a matsayin sharadin da likita ya gindaya masa kafin ya duba shi.

KU KARANTA: Dubun wasu ɓarayi ta cika, Anyi musu ɗaurin demon minti (Hotuna)

Kaakakin yace yansanda sun gano hakan ne yayin da suka yi masa yan tambayoyi kan yadda yaji raunin, inda daga bisani suka fahimci ya jiyo raunin ne sa’ailin da yake yi ma wata yarinyar fyade.

Kurungus! Ta yi masa kaciya, bayan yayi mata fyaɗe
Yansanda

Wannan mummunan lamari, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito ya faru ne a garin Kankara a ranar 15 ga watan Mayun data gabata.

Daga karshe Alkalin Kotun, mai shari’a Fadile Dikko ya bada umarnin a tasa keyar mutumin zuwa gidan Kurkuku, sa’annan ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Yuli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel