Lokaci Ya Yi: Yayan Tsohon Gwamnan Sokoto, Liman Tambari Ya Rasu
- Allah ya yi wa yayan tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko, rasuwa a ranar Lahadi, 28 ga watan Afirilun 2024
- Marigayi Alhaji Liman Tambari Wamakko ya rasu ne asibitin koyarwa na jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto bayan ƴar gajeruwar jinya
- Jana'izar marigayin ta samu halartar gwamnan jihar, Ahmed Aliyu Sokoto, kakakin majalisar dokokin jihar da sauran masu faɗa a ji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Yayan Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Alhaji Liman Tambari Wamakko, ya rasu a daren Lahadi a Sokoto.
Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi a asibitin koyarwa na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto sakamakon gajeruwar rashin lafiya.
Babban limamin masallacin Wamakko, Liman Shehu Ardo Wamakko ne ya jagoranci sallar jana'izar marigayi Liman Tambari, mai ba taimakawa sanatan kan harkokin yaɗa labarai ya bayyana hakan a wata sanarwa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sallar jana'izar ta samu halartar ƙanin marigayin, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto, Tukur Bala Bodinga.
Sauran sun haɗa da sakataren gwamnatin jihar, Muhammadu Bello Sifawa, da tsohon ministan harkokin ƴan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi da sauran manyan mutane a jihar.
Wamakko ya yi jimamin rasuwar
Jim kaɗan bayan kammala sallar jana'izar, Sanata Aliyu Wamakko ya yi bayanin cewa tabbas babu makawa sai an bar duniyar nan.
Ya bayyana cewa kowane mai rai zai ɗanɗana mutuwa idan lokacinsa yayi.
Sanatan ya tuna baya cewa su 11 ne aka haifa ciki har da marigayi Liman Tambari, amma yanzu su uku kawai suka rage a duniya.
Ya yi addu'ar Allah maɗaukakin Sarki ya yafe masa kura-kuransa sannan ya sanya Aljannah ta zama makoma a gare shi.
Sanata Wamakko ya kuma miƙa godiyarsa ga duk waɗanda suka halarci jana'izar babban ƴaƴan nasa, tare da yin addu'ar Allah ya saka musu da alheri.
Tsohon gwanman Yobe ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Allah ya yi wa tsohon gwamnan jihar Yobe, Aƙhaji Bukar Abba Ibrahim rasuwa a ƙasar Saudiyya.
Marigayi tsohon gwamnan ya yi bankwana da duniya ne yana shekara 73 bayan ya yi fama da jinya a ƙasa mai tsarki kwanaki.
Asali: Legit.ng