Mummunan Hatsarin Mota Ya Salwantar da Rayukan Mutum 19 a Kogi

Mummunan Hatsarin Mota Ya Salwantar da Rayukan Mutum 19 a Kogi

  • Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Kogi ya yi sanadiyyar salwantar da rayukan mutum 19 har lahira
  • Hatsarin motan ya auku ne bayan wata motar Dangote ta yi taho-mu-gama da wata motar bas mai ɗauke da fasinjohi
  • Sanarwar da kakakin hukumar FRSC a jihar ya fitar ta tabbatar da cewa mutanen sun rasa ransu bayan gobara ta tashi sakamakon hatsarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Fasinjoji 19 sun rasa ransu bayan sun ƙone a wani hatsarin mota kan hanyar Okene-Lokoja a jihar Kogi

Hatsarin motar ya ritsa ne da wata motar Dangote mai lamba NSH680YJ tare da wata motar bas ƙirar Toyota Hiace mai lamba KMC455ZE.

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin sama ta ragargaji 'yan ta'adda a jihar Neja

An yi hatsarin mota a Kogi
Hatsarin mota ya salwantar da rayukan mutum 19 a Kogi Hoto: @FRSCNigeria
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), Jonas Agwu, ya fitar, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hatsarin motan ya auku

A cewar sanarwar motocin biyu sun yi taho-mu-gama ne bayan motar Dangote ta sha gaban motar da ke gabanta ba daidai ba, wanda hakan ya haifar da tashin gobara.

Hukumar ta ce daga cikin fasinjoji 22 da hatsarin ya ritsa da su, an ceto mutum uku da ransu, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Motar bas ɗin wacce ta yi lodi daga Kano tana kan hannunta lokacin da motar Dangote da ta taso daga Fatakwal ta wuce wata mota ba daidai ba, wanda hakan ya sanya suka yi taho mu gama."
"Taho-mu-gaman da suka yi, ya yi sanadiyyar tashin gobara wacce ta ƙona mutanen."

Kara karanta wannan

Bam ya hallaka jami'an CJTF 5 a jihar Borno, wasu sun samu raunuka

"Abin takaici, 19 daga cikin mutanen da hatsarin ya shafa sun rasu, yayin da guda ɗaya ya samu rauni. Sauran mutum biyun da jami'an FRSS suka ceto ba su samu rauni ba saboda sun bi ƙa'idojin tuƙi."

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa rayukan mutum 10 sun salwanta bayan motar da suke ciki ta gamu da mummunan hatsari a jihar Kaduna.

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta ce fasinjoji 10 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya ritsa da wata motar tirela

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng