Yadda Gidauniyar Al Masaakin Ta Ciyar da Mutane 8000 a Ramadan da Karo Karo
Al-Masaakin Charity Foundation gidauniya ce da ke tallafawa marasa karfi wajen samun jari, abinci, kiwon lafiya, ruwa da makaranta.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Legit Hausa ta zanta da Waleed Abdullahi wanda babban jami’in da ke kula da Al-Masaakin ne domin jin irin kokarin da suke yi.
Abin ban sha'awar shi ne daidaikun mutane ne suke ba gidauniyar dukiyar yin aiki.
Hira da jami'in gidauniyar Al-Masaakin
Legit: Me za ku ku fada mana game da Al-Masaakin?
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A takaice, Al-Masaakin Charity Foundation ta fara aiki ne a shekarar 2015 a Kaduna bayan wadanda suka kafa ta sun ga bukatar kawo tsarin raba abinci na FeedAMouth. Da aka yi nasara, sai aka fito da yunkurin zuwa ga sauran al’umma.
Zuwa 2016 sai Al-Masaakin Charity Foundation ta samu rajista da hukumar CAC a karkashin shugabanni biyar a karkashin jagorancin shugabanta.
Mun gode Allah SWT, a yau wannan aiki ya shiga jihohin tarayya 16 kuma ta na kara gaba.
Legit: Mecece manufar Al-Masaakin?
Manufarmu ita ce jajircewa wajen ba da tallafi ga mutane ba tare da la’akari da kabilanci, sharadi ko wani son kai ba.
Burinmu shi ne samar da kamfanin da zai taimaka wajen ganin mutane sun yi amfani da dukiyarsu a kan al’umma.
Legit: Ta ina ku ke samun kudin gudanar da al’amura a AL?
Al-Masaakin Charity Foundation tana samun gudumuwa ne daga daidaikun mutane da suka ware kaso daga albashinsu na wata domin aikin Allah SWT, da masu ba da zakkah sai kuma masu daukar nauyin ayyukan ciyawarwa, samar da ruwa, tara kudin asibiti da tallafin Ramadan.
Legit: Ya tsarin Ramadan yake?
Al-masaakin ta samar da tsare-tsare na watan Ramadan irinsu:
1. Ciyarwa
2. Samar da hanyar ruwan sha a watan azumi
3. Ziyara zuwa asibitoci da biyan kudin magani
4. Tallafawa da jarin kasuwanci
5. Sauran ayyuka irinsu kacici-kacici
Legit: Ta ya ake daukar mutane aikin Al-Masaakin?
Da zarar an bude kafar masu aikin sa’kai, muna tallatawa ta dandalin sada zumuntan zamani sai mutane sun ema gurabe daga jihohi 19 da mu ke aiki. Bayan sun yi rajista, mu kan tantance su domin zama cikakkun ‘yan kungiya.
Legit: Ko akwai nasarorin da aka samu zuwa yau?
Da yardar Allah SWT mun cin ma nasarori daga raba dafaffe da tsabar abinci ga mutane sama da miliyan biyu, an gina rijiyoyi akalla 2000, akwai marayu 14 a karkashinmu a Kaduna, akwai zaurawa da maza marasa karfi har fiye da 100 da muka ba tallafi. Sannan mu na kai ziyara duk wata zuwa asibitoci.
Tasirin Al-Masaakin a jihohin Najeriya
Burin gidauniyar Al-Masaakin ita ce kawo cigaba a al’umma ta hanyar ba da ilmi, tallafi da sauran tsare-tsaren da za a yi alfahari da su.
Al-Masaakin ta shaidawa Legit cewa a watan Ramadan da ta gabata, sun ciyar da abinci ga mutane 8, 366 a jihohi kusan 20 a kasar nan.
Auren 'ya 'yan Sarakuna a Kano
Yayin da ake ta daurin aure, an ji labarin yadda daya daga cikin 'ya 'yan Sarkin Kano ya nemi auren diyar Sarkin Bichi a karshen makon nan.
Sanusi Aminu Bayero ya zama mai gidan Rumana Nasir Ado Bayero. Dama auren zumunci ba bakon abu ba ne, ya shahara a yankin Arewa.
Asali: Legit.ng